Ƙorafi game da yaƙi da cin hanci a Nijar
August 23, 2011Talla
Ƙungiyoyi daban-daban na Jamhuriyar Nijar sun bayyana rashin amincewarsu dangane da abinda suka kira son kai da gwamnati ke nunawa cikin yaƙi da ta ke yi da almundahana da kuma yin katsalandan cikin harkar shari'ar waɗanda aka zarga da wannan ɗanyen aiki. Waɗannan ƙungiyoyin da suka haɗa da na ƙawancen ƙungiyoyin ma'aikatan baitil mali da kuma na ma'aikatar kuɗi na kasa, da kuma ƙungiyar alƙalan Nijar sun yi waɗannan korafe-korafe ne a cikin sanarwa da kowacce su ta fitar a birnin Yamai.
Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Mouhamadou Awal