Ƙalubale ga hukumar INEC a Najeriya
February 22, 2011Talla
A Najeriya 'yan siyasa da ƙungiyoyi masu zaman kansu na cigaba da baiyana martani a game da sunayen mutane 20 da hukumar zaɓe ta ƙasar INEC ta amince cewa sune za su shiga takarar neman kujerar shugabancin Najeriyar a zaɓen da za'a yi a cikin watan Aprilu mai zuwa.
A waje guda kuma Jam'iyar adawa ta ANC ta soki lamirin jam'iyar PDP mai mulki tare da hukumar zaɓen ta ƙasa bisa amfani da tsohon tsarin zaɓe wanda ta ce wani shiri ne na yin maguɗi a zaɓen dake tafe
Mawallafa: Uwais Abubakar Idris/Mansur Bala Bello
Edita: Abdullahi Tanko Bala