Ziyarar shugaban Nijar a tarayyar Jamus
May 8, 2013Talla
Kafin ganawarsa da Merkel, shugaba Issoufou zai tattauna ne da ministan raya kasashen ketare na Jamus Dirk Niebel kuma ana sa ran tattaunawar ta su za ta fi maida hankali kan halin da ake ciki a makociyar Jamhuriyar Nijar wato Mali wadda ke fama da rikici kazalika shugabannin biyu za su tattauna dangane da halin da tsaro ke ciki a yankin Sahel baki daya.
Jamus dai na zaman guda daga cikin kasashen duniya da ta dade ta na hulda irin ta raya kasa da Jamhuriyar Nijar inda mahukutun kasar su ka yabawa Nijar din dangane da gyare-gyaren da ta yi game da tsarin demokradiyya a kasar da kare hakkin bil adama da 'yancin fadin albarkacin baki da kuma kawar cin hanci da rashawa.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu