Ziyarar Obama ga nahiyar Turai
May 20, 2011Ajendar taron dai ta ƙunshi batutuwa ne na tattalin arzƙin duniya da sauran batutuwa na ƙasa da ƙasa kamar dai halin da ake ciki a ƙasashen Larabawa. A zamanin baya dai ana sha nuna ɗoki da ziyarar shugaban na Amirka a nahiyar Turai, amma a yanzu tuni murna ta koma ciki dangane da fatan da aka yi cewar Obama zai kawo canji ga dangantakar Amirka da sauran sassa na duniya.
An saurara daga bakin shugaban Amirkan a shekara ta 2009 yana mai faɗin cewar:
"A haƙiƙa an samu saɓani a dangantakar Amirka da ƙasashen Turai a cikin shekaru bakwai zuwa takwas da suka gabata, amma babbar manufar gwamnatina ita ce ta sabunta wannan dangantaka ta tarihi dake tsakanin sassan biyu."
Sau shida shugaban na Amirka na kawo ziyara nahiyar Turai tun a cikin shekararsa ta farko da kama ofis. Kuma a duk inda ka waiwaya zaka tarar an yi cincirindo a cikin ɗoki da murna don yi masa marhaban ta sha tara ta arziƙi. Amma a halin da ake ciki yanzu tuni wannan murna ta koma ciki. An saurara daga farfesa Werner Weidenfelder mai koyar da kimiyar siyasa a jami'ar München, wanda ya daɗe yana bin diddigin dangantakar ƙasashen arewacin tekun atlantika yana mai bayanin cewar:
"Sake farfaɗo da dangantakar domin komawa kan sibgarta ta asali a fannin tsaro da haɗin kai akan dukkan batutuwan da suka shafi siyasar duniya, abu ne dake buƙatar himma da ƙwazo da ma aiki tuƙuru fiye da abin da aka gani daga ɓangarin Amirkan da nahiyar Turai ya zuwa yanzu."
Hakan na faruwa duk kuwa da lasar takobin da dukkan sassan biyu ke yi game da bin wannan manufa akan duk matsalolin da suka shafi dangantakar ƙasa da ƙasa. An ma ji daga bakin sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton tana mai bayani dangane da wannan ziyara ta Obama cewar:
"Akwai ƙaƙƙarfan ƙawance tsakanin Amirka da ƙungiyar tarayyar Turai. Muna haɗin kai a dukkan batutuwan da suka shafi al'amuran duniya da kuma rikice-rikice na yankuna. Kazalika aiki tare akan dukkan matsaloli masu muhimmanci bisa turbar gamayyarmu ta ƙasashen arewacin tekun atlantika, waɗanda ke fatan tabbatar da kyakkyawan tsari na demokraɗiyya dake ba wa ɗan Adam 'yanci da walwala."
To sai dai kuma akwai banbanci a salon tunani game da waɗannan manufofin tsakanin Amirka da nahiyar Turai, kamar ma dai yadda aka gani dangane da rikicin Libiya. Kazalika ma dai da ayyukan kiyaye zaman lafiya a ƙasar Afghanistan, inda ake samun banbance-banbance tsakanin sassa biyu dangane da yadda za a tinkari matsalar. Wannan ziyarar ta Obama a ƙasashen Turai dai ta zo ne daidai lokacin da ƙasashen ke fama da matsaloli na siyasa sakamakon ɗimbim bashin dake addabar wasu daga cikin ƙasashen ƙungiyar tarayyar Turai. Shugaban na Amirka dai ba zai kai ziyara shelkwatar ƙungiyar a Brussels ba, kazalika ba zai ya da zango a Jamus ba. A baya ga Faransa, ziyarar zata kai shi ne zuwa ƙasashen Irland da Birtaniya da kuma Polen ko da yake ko shakka babu za a yi musayar miyau tsakaninsa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel lokacin taron ƙolin ƙasashen gamayyar ta G8 a Deauville ta ƙasar Faransa.
Mawallafi: Daniel Scheschkewitz/Ahmad Tijani Lawal
Edita: Mohammed Nasiru Awal