Zelensky da Trump sun fara ganawa a fadar White House
August 18, 2025Shugaban Amurka Donald Trump ya tarbi takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky a fadar White House a maraicen wannan Litinin, inda suka fara tattaunawa mai zurfi kan yiwuwar cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Rasha.
Gabannin wannan ganawa mai cike da tarihi, Trump ya ce idan komai ya tafi yadda ya kamata zai shirya wata haduwa nan gaba a tsakaninsa da Putin da kuma Zelensky, matakin da shugaban Ukraine ya ce a shirye yake ya amince da shi muddin za a kawo karshen mamayar da Rasha ke yi wa kasarsa.
Karin bayani: Kasashen Turai na matsin lamba ga Amurka kan tabbatar da tsaron Ukraine
Hakazalika shugaba Trump ya yi alkawarin cewa Amurka za ta ba da gudummowa sosai a harkokin tsaron Ukraine muddin aka yi nasarar kawo karshen rikicinta da Rasha.
Ana sa ran wannan taron gaggawa na ranar Litinin zai dora dan ba kan makomar Ukraine, duk da dai kasashen Turai na fargabar a yi wa Kiev matsin lamba domin amincewa da yarjejeniyar da Rasha kadai ka iya cin gajiya.