SiyasaAfirka
Zelenskiy na neman hadin kan Afirka ta Kudu a yakin Ukraine
April 24, 2025Talla
Shugaba Zelenskiy na ta fadi tashin ganin ya samu hadin kan shugabannin kasashen duniya a yakin da kasar ke gwabzawa da Rasha, a daidai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da Zelenskiy cewa in bai bada kai bori ya hau ba, to babu shakka zai tsame kan sa daga shirgin yakin Ukraine.
Karin bayani: Kasashen Afirka na kokarin sulhunta fadan Rasha da Ukraine
Kasar Afirka ta Kudu na da kyakkyawar alakar diflomasiyya da Rasha, kuma ta ki goyon bayan kowanne bangare a yakin Ukraine. Hukumomin Pretoria sun sanar da cewa shugaba Ramaposa ya tattauna ta wayar tarho da Vladimir Putin na Rasha a ranar Litinin gabanin ziyarar Zelenskiy inda suka sha alwashin tafiya da murya daya wajen kawo karshen yakin da kuma hadin kan kasashen.