Zaɓen shugaban ƙasa a Chadi
April 25, 2011A yau al'umar ƙasar Chadi ke kaɗa ƙuri'a a zagayen farko na zaɓen shugaban ƙasa inda shugaba mai ci Idriss Deby Itino ke fatan cigaba da tazarce bayan shafe shekaru 21 akan karagar mulki.
'Yan takarar adawa waɗanda suka haɗa da Saleh Kebzabo da Wadal Abdelkader da kuma Ngarlejy Yorongar sun janye daga zaɓen ne wanda suka baiyana da cewa kulli kurciya ce kawai, suka kuma buƙaci magoya bayansu da suma su yi hakan. Jam'iyyun adawar dai sun buƙaci gudanar da gyare gyare gabanin zaɓen wanda ya haɗa da sabunta katin rajistar masu zaɓe sun yi ƙorafin jam'iyyar Idris Deby ta yi amfani da katunan wajen yin maguɗi a zaɓen majalisar dokoki da aka gudanar a watan Fabrairu. A waje guda dai shugaba Idris Deby ya yi kira ga yan ƙasar ta Chadi da su haɗa kai su kuma manta da dukkan wasu banbance-banbancen dake tsakanin su.
Wannan dai shine karo na huɗu da shugaba Deby ke yin tazarace tun lokacin da ya dare karagar mulki bayan juyin mulkin da ya hamɓarar da gwamnatin Hissen Habre a shekarar 1990. Wakilin mu a birnin Njamena Abdulrazak Garba Baba Ani yace jama'a basu fito ba sosai a zaɓen na yau idan aka kwatanta da sauran zaɓɓukan da suka gudana a baya. 'Yan ƙasar Chadi miliyan huɗu da dubu ɗari takwas ne daga cikin al'umar ƙasar miliyan goma sha ɗaya ake sa ran za su kaɗa ƙuri'a a zaɓen na yau.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Yahouza Sadissou Madobi