Zaɓen majalisar dokoki a Chadi
February 11, 2011A bayan shirye-shirye na lokaci mai tsawo da kampe na jan hankalin jama'a, al'ummar kasar Chadi zasu sami damar kada kuri'un su a zaben majalisar dokoki ranar Lahadi. Wannan zabe ana ganin sa kamar dai gwaji ne a kokarin da yan adawa suke yi na ganin sun kawar da mulkin shugaban kasa Idriss Derby, idan aka zo zaben shugaban kasa nan gaba a wannan shekara. Kungiyar hadin kan Turai da ta tura yan kallo kimanin 70 wadanda zasu lura da yadda zaben zai gudana, ta sanar da cewar yan takara akalla 1400 ne daga jam'iyu masu akidodi iri dabam dabam suke neman kujeru 188 a majalisar dokokin kasar ta Chadi.
Shekaru tara da suka wuce, lokacin zaben majalisar dokoki na karshe da aka yi a kasar, jam'iyar Derby ta MPS ce ta kwashe kashi biyu cikin kashi ukku na kujerun majalisar. Sai dai kuma jim kadan kafin zaben na bana, Derby ya sallami shugaban hukumar zabe, abin da ya sanya yan adawa suke korafin cewar akwai shirye-shirye na magudi a wannan zabe. Gaba daya mutane miliyan hudu da digo takwas ne aka yi rajistar su a zaben na ranar Lahadi.
Wakilin mu a Ndjamena, babban birnin kasar ta Chadi, Abdoulrazak Garba Baba Ani, ya tanadar mana da rahotanni da suka shafi zaben, tun daga matsayin yan takara da yadda talakawa suke kallon masu neman kuri'un su da yadda arzikin man fetur da take dashi ya shafi zaman jama'a da kokarin kungiyar hadin kan Turai na baiwa Chadin taimako domin ganin zaben ya gudana lami-lafiya ba tare da magudi ba.
Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita Abdullahi Tanko Bala