SiyasaAsiya
Zargin yada bidi'a ya sa Musulmin Karachi kashe dan Ahmadiya
April 18, 2025Talla
Daruruwan Musulmi da ke da tsatsauran ra'ayi sun kashe wani mutum har lahira a kudancin Pakistan bisa zarginsa da yada bidi'a saboda yana bin tafarkin darikar Ahmadiyya. Tun dai bayan da Pakistan ta mayar da Islama a matsayin addinin kasa bayan rabuwa da Indiya ne, 'yan Ahmadiyya ke fuskantar kyama daga sauran Musulmi saboda imanin da suka yi da zuwan wani annabi bayan annabi Muhammadu SAW.
Kundin tsarin mulkin kasar Pakistan ya ayyana 'yan Ahmadiyya a matsayin wadanda ba musulmi ba tun a shekarar 1974, kuma wata doka ta hana su yada akidarsu tun shekaru 41 da suka gabata. Sai dai taruwa da 'yan Ahmadiyan suka yi a wannan Jumma'ar a wurin ibadarsu a birnin Karachi ne ya sa masu kishin Islama 600 yi musu kawanya tare da far musu.