Zargin bangarenci a nada mukamai a Najeriya
April 9, 2025.
Kama daga kamfanin mai na kasar ya zuwa babban banki gami da muhimman kaddarori na kasar dai duk sun koma a karkashi na shugabanci na kabila guda daya a tarayyar Najeriya a halin yanzu. Abin kuma da ke tada hankali cikin gidan jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya da 'yan jam'iyar ke fadin da sauran sake.
Karin Bayani: Fargabar dorewar dimukuradiyya a Najeriya
Wani jigon jam'iyyar, kuma dan majalisar dattawa ne dai ya fara jawo hankalin Shugaba Bola Ahmed Tinub na Najeriya bisa tsarin nadin da ke zaman ba sabunba. Sanata Ali Ndume dai ya zargi shugaba Tinubu da karen tsaye cikin kundin tsarin mulkin kasar.
To sai dai kuma akwai alamun Ndume na fadi da yawun da dama cikin gidan jam'iyyar da daga duk na alamu 'ya'yanta ke ta kara korafi bisa rawa ta shugaban. Abdurahaman Baffa Yola dai na zaman tsohon mashawarcin siyasa ga tsohon mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo, kuma jigo a cikin jam'iyyar APC wanda ya bayyana cewa ana bukatar adalci domin tabbatar da smaun hadin kai tsakanin 'yan kasar.
A yayin da jihar Ogun ta zamo ta kan gaba cikin samun mukamai a tsohuwa ta gwamnati ta Buhari, jihar Lagos ce ta dauki hankalin Tinubu kuma ta samu mafi yawa na mukamai na shugaban. Kuma ko bayan nan dai ya zuwa yanzun kusan kaso 60 cikin dari na daukacin mukaman gwamnatin Tinubu dai sun fito ne daga yankinsa na kudu maso yamma. Bakar siyasar iko ko kuma gwagwarmaya ta neman aci dai, ana dai kallon sabuwar gwagwarmayar cikin gidan jam'iyyar APC dai na nuna alamun rikicin da ke gaban jam'iyyar.