Rikice-rikiceJamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango
Kwango: Bude wuta kan masu zanga-zanga
September 8, 2025Talla
A cewarsu sojan da ake zargin na goyon bayan 'yan tawayen da ke samun Ruwanda ke marawa baya, sun bude wuta kan masu zanga-zangar lumanar da ba sa dauke da makamai a birnin Uvira da ke Kivu ta Kudu tare da halaka kimanin mutane hudu da kuma jikkata wasu guda bakwai. Sai dai gwamnan Kivu ta Kudun Jean-Jacques Purusi Sadiki ya nunar da cewa, a hukumance mutane uku ne suka tabbatar sun rasa rayukansu kana wasu biyar suka jikkata. Duk da cewa ya yi ta'aziyya ga dangin mamatan da ya ce suna zanga-zanga ne ba tare da daukar makamai ba, sai dai yaki furta komai a kan wanda ko wadanda suka bude musu wutar.