Zargin cin hanci a tantance ministocin Ghana
January 29, 2025A kasar Ghana an kammala sauraron bayanin wani dan rajin yaki da rashawa a kasar wanda ya yi amai ya lashe, bayan zargin kwamitin majalisar dokokin kasar da ke kan aikin tantance ministoci da karban rashawa. Zargin da ya tilasta majalisar dage zama a ranar Talata, kuma ta bukaci Oliver Barker Vormawor ya gurfana a gaban kwamitin ranar Laraba, kuma ya yi bayani dalla-dalla kamin a ci gaba da sauran aikin tantance ministocin.
Karin Bayani: Ghana: Shugaba Mahama ya nada ministoci 42
Sau biyu ne aka wallafa zargin a shafin sada zumunta na Oliver Barker Vormawor, na farko a ranar 24, na biyu a ranar 25 ga watan Janairu, wanda ya amince da cewa shi ne ya wallafa kuma ya yi yaduwan wutar daji a shafukan sada zumunta a kasar, sai dai na farkon jabu ne. Acewar lauyansa Nana Ato Dadzie, wallafin ba wani yunkuri ba ne na sukar kwamitin tantance ministocin kai tsaye.
Patricia Apiagyei mataimakiyar jagoran bangaren adawar gwamnati a majalisar dokoki da ke wakiltan mazabar Asoka a jihar Ashantin Ghana, ta yi tir da lamarin jim kadan bayan zaman, inda masana ke kwatancin wannan wani darasin koyi da yin dubiya kan 'yancin fadan albarkacin baki bisa la'akari da lokacin da ya dace.