SiyasaTurai
Zanga-zangar yaki da cin hanci a Ukraine
July 31, 2025Talla
Majalisar dokokin kasar Ukraine a wannan Alhamis ta amince da dokar da ta sake dawo da 'yancin cin gashin kai ga hukumomin yaki da cin hanci da rasha na kasar guda biyu, sakamakon zanga-zanga da aka fuskanta a kasar. Shugaba Volodymyr Zelensky na kasar ta Ukraine ya mika wa majalisar neman amincewa da kudirin dokar bayan wannan zanga-zanga.
Karin Bayani: Kasashen duniya na shirin samar da kudaden sake gina Ukraine
Masu zanga-zangar sun fusata sakamakon yadda ake sako-sako da batun yaki da cin hanci da rasha tsakanin masu karfin fada aji na kasar ta Ukraine. Tun shekara ta 2015 aka amince da kafa hukumomin domin yaki da cin hanci tsakanin manyan jami'an gwamnati da jiga-jigan 'yan siyasa sakamakon matsin lamba daga manyan kasashen duniya.