Zanga zangar goyon bayan ficewar Nijar daga kungiyar ECOWAS
January 28, 2025Makasudin taron gangamin dai shi ne kawo goyon baya ga shugabannin kasashen kungiyar AES na Nijar Mali da Burkina Faso da kuma nuna adawa ga ci gaba da amfani da kudin CFA a cikin kasashen AES.
Dubun-dubatar ‘yan Nijar ne dai maza da mata suka hallara a wannan rana ta 28 ga watan janerun 2025 domin kawo goyon bayansu ga shugabannin kasashen AES na Nijar, Mali da Burkina Faso, a daidai loakcin da ya rage sa'oi kalilan wa'adin da kasashen suka dauka na ficewa daga kungiyar ECOWAS bayan shekaru 50 a cikinta ke cika.Malama Falmata Taya na daya daga cikin shugabannin kungiyar M62 daya daga cikin kungiyoyin da suka shirya wannan taron gangami.
"Biki ne muke yi na tabbatar wa da duniya cewa matakin da kasashenmu suka dauka na ficewa daga ECOWAS babu zancen dawowa baya. Kungiyar CEDEAO ta zamo tarihi domin mu a yanzu AES muke yi. Kuma wannan biki a yau ana yin irinsa a Mali da a Burkina Faso. Mu duka mu gama karfi da karfe mu take wa shugabannin baya saboda wannan tafiya, tafiya ce da ake yi don kasa don amfanin al'umma. Muna kira ga sauran kasashen Afirka da suke cikin kangin Turawa, su zo su shigo AES yau it ace mafita"
Taron gangamin wanda kuma ke da nufin nuna adawa da ci gaba da amfani da kudin CFA a cikin kasashen na AES ya samu halartar dubban matasa maza da mata daga lunguna da sakon na birnin na Captain Salma.
"Idan ka dubi kudin CFA a matakin daraktar kudade a duniya ana kallonsu ne a matsayin takarda ba kudi ba. Kuma wadannan kudade suna daga cikin abubuwan da ke kawo mana koma baya a cikin tattalin arzikin kasashenmu. Shi ya sa a yau muka fito muke nuna wa magabata maganar kudin nan na CFA shi ma su mayar da hankali kanshi su yi kokari su samar da kudi namu na kanmu nan ba da jimawa ba domin kawo karshen amfani da wannan kudi"
Sai dai ko a cikin birnin Yamai akwai wadanda suka kaurace wa taron suna masu nuna adawa da matakin ficewar kasar ta Nijar daga cikin ECOWAS , Malam Sahnin Mahamadou na daga cikin masu wannan adawa.
"Allah wadaran naka ya lalalce in ji rakumin dawa da ya ga na gida. Domin wadannan mutanen da suka fito suke zanga-zangar goyon bayan ficewa daga CEDEAO da sun san hadarin da suke taimaka wa wadannan sojoji saka kasarmu ciki to da sun ja da ba. Kuma ya kamata al'ummar Nijar ta gode wa kasashen ECOWAS kamar Najeriya da Benin domin shugabanninsu suna tausayin talakawan mu shi ya sa basa biya ta wadannan sojoji, suke kyalewa ana yin wasu abubuwa. Kuma sun yi imanin cewa abin da ke faruwa al'ummominmu basu yarda da shi ba. Illa iyaka an fi karfinsu ne ana amfani da tsinin bindiga ana tursasa su.
Taron gangamin wanda ya samu halartar wasu daga cikin shugabannin majalisar koli ta sojojin Nijar ya wakana lami lafiya inda daga karshe aka yi ta cashewa da wakokin na yabon sojojin kasar ta Nijar.