Zanga-zangar dalibai a fadin Jamhuriyar Nijar
December 15, 2011
Yau ne a fadin kasar jamahuriyar Nijar 'yan makaranta sukayi
zanga-zangar ta gama gari, domin nuna bakin cikin su ga gwamnati
dangane da rasuwar yan uwan su na birnin Zinder da kuma wasu matsaloli
da suke fuskanta.
A fuskar jihar Tahoua dai yan makarantar na sakandre tare da daliban
jami'a sun yi jerin gwanon ne har ya zuwa offishin gomnan jihar Tahoua,
inda suke kiran sai shari'a ta yi aikin ta dangane da kashe abokan su
da raunana wasu da dama da aka yi a baya bayan nan, a birnin Zinder da
Diffa dake gabacin kasar. Cikin koken na su yan makatantar sun yi fatan
ganin an sasanta da malamen kontaragi don ganin sun samu ci gaban
karatun su, inda daya daga daliban ke cewa
"Sunana Salissou Ibrahim malam Umaru mun fito ne
domin mu tuna wa gomnati cewa muna jiran shari'a ta yi aikin ta maluman
mu suna yajin aiki gwamnati ta sasanta da su"
"Ita kuwa wata yar makarantar cewa take: Tun ba'a haife mu ba ake batun neman shari'a ga
wasu dalibai da aka kashe, kuma gashi yanzu an samu wasu kuma da suka
rasu sakamakon harbin da yan sanda suka yi a Zinder da Diffa dan haka
muna jiran sakamakon shari'a"
Ganin cewa wannan jerin gwano na kasa baki daya ne, da babbar kungiyar
yan makarantar da ta daliban jami'a ta birnin Yamai ta kasa ta kira,
inda suma a nan Tahoua daliban sunyi nasu bayannai a gaban gwamnan jiha
inda suke cewa ..
"Dangane da farashin man petur da gwamnati ta tsaida, wanda kuma
babbar kungiyar mu ta dalibai na Nijar muka yi watsi da shi, dangane
da ganin yadda karatun boko na shekara ta 2011 izuwa 2012 yake fuskantar
babban kalubane, dangance da halin dandana kuda da al'ummar kasa ke
ciki, dangane da tsadar rayuwa, mu daliban jami'ar birnin Tahoua ke kira
ga gwamnati da ta dubi harkokin makantu da idon rahama tare da ganin
shari'a ta yi aikin ta" Kazalika daliban sun yi kira ga gwamnati da ta rage
kudin farashin man fetur.
Da yake bada amsa ga daliban,gwamnan jihar Tahoua Amadu Ide ya
jinjinawa daliban na Tahoua ganin yadda suka gudanar da jerin gwanon
nasu cikin lumana yana mai cewa…
"Kamar yau da kullun da nake fada, mu a nan Tahoua kofofin mu a bude
suke kuma a shirye muke domin mu tattauna kan duk wasu matsaloli da
suka shafe mu kuma zamuyi maganin wadanda suke karkashin ikon mu bakin
gwargwado, sannan wadanda suka fi karfin mu, zamu sanar da magabatan mu
kuma mu bi sau da kafa"
Bisa yadda yan makarantar ke kokawa da yajin aikin maluman su, magatakardan kungiyar malamen makaranta yan kontaragi na jihar Tahoua Mahamed Yatan yace…
"Yau yara sune ke amfani da karatun da muke badawa to yau gashi
sun fito sunce basa samun karatu, don haka kenan ya kyautu duk wadanda
nauyin sanar da mahakumta na koli ya rataya a kansu, su rinka gaya musu
gaskiya domin hakan na nuna cewa yajin aikin da muke yi, yana karbuwa tun
yaran da kan su sun fada matsala ce fannin ilimi idan har ana so a yi
gyara."
Wannan karon dai, daliban na dukkan makarantu ne suka fito na gwamnati
da masu zaman kansu, domin amsa kiran babbar kungiyar dalibai ta kasa
dake neman gwamnati ta ji kukanta da ma na yan kasa baki daya.
Mawallafa: Salissou Boukari da Halima Balaraba Abbas
Edita: Usman Shehu Usman