Ko hankalin matasan Afirka ya koma gona?
September 3, 2025Kasar Zambiya na ci gaba da samun karuwar alkaluman matasan da suke zaman kashe wando, saboda rashin ayyukan yi na gwamnati. Phingiwe Musende matashiya ce da ta samu horo na aikin jinya, sai dai kuma har yanzu babu aikin yi. Abin da ya sanya, ta rungumi sana'ar na duke tsohon ciniki. Duk da cewa maza ne suka yi kane-kane a wannan sana'ar a Zambiya, a yanzu ta zama kallabi tsakanin rawuna. Ita dai wannan matashi ta fara sana'ar ce daga wani dan karamin lambu na kayan ganye, wanda sannu a hankali yake rikidewa zuwa gona. Musende ta samu kai wa ga wannan nasara ce tare da taimakon mai gidanta, Simon Bwalya wanda suke aiki tare. Ya ce, tallafin da yake bai wa matarsa a harkar noma ya sauya rayuwarsu matuka.
Shi ma dai matashi Andrew Machila wanda ke zaune kusa da birnin Lusaka, ya yanke shawarar barin aikinsa a matsayin mai sanya ido a wani kamfani da ke harkar fitar da kaya daga kasar. Yana ganin abin da ake biyan sa bai taka kara ya karya ba, a yanzu dai Andrew ya koma harkar ta tushen arziki. To sai dai ko ga tsofaffin manoma a kasar, kusan kaso 60 cikin 100 na manoman na fuskantar koma-baya a harkar saboda karancin masu siyan amfanin gonan da kuma ci-gaban fasaha. Sai dai Musende da kuma Machila na taimaka wa wajen sauya hakan ta hanyar amfani da kafafen sada zumunta wajen tallata kayansu da ma samar da guraben ayyukan yi ga sauran matasa. A yanzu dai matasan Zambiya da suka gano sirrin naduke tsohon ciniki na fatan ganin gwamnatin kasar ta zuba jari a harkar tare da karin tallafi, domin bunkasa harkar da ma rayuwar su matasan.