Amurka da Iran za su ci gaba da tattaunawa
April 17, 2025Shugaban hukumar kula da makamashi ta Majalisar Dinkin Duniya, Rafael Grossi ya bayyana kasar hukumar za ta taka rawa yayin zagaye na biyu na tattaunawa tsakanin kasashen Iran da Amurka, kan hanyoyin dakile bunkasa makamashin nukiyar Iran. Shi dai Grossi ya bayyana haka lokacin ziyara a birnin Tehran fadar gwamnatin kasar Iran, inda ya tattauna da jami'an gwamnatin kasar ciki har da ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi.
Karin Bayani: Shugaban IAEA ya ce Iran na daf da mallakar makamin nukiliya
Ana sa ran ci gaba da taattaunawar ranar Asabar mai zuwa a birnin Rome na kasar Italiya tsakanin wakilan bangarorin Amurka da Iran gami da kasra Oman mai shiga tsakani.
Ana fata kan wannan tattaunawa za ta bude hanyar dakile kasar Iran daga samun makamun nukiliya, yayin da a daya bangaren za a sassauta takunkumin karya tattalin arzikin da aka saka kan kasar.