SiyasaAfirka
Zaftarewar kasa ta halaka mutane sama da dubu a Sudan
September 2, 2025Talla
Zaftarewar kasar ta shafe kauyen Tarasin da ke kusa da tsaunukan Marra a lardin Darfur, inda ya halaka mutanen da ke kauyen baki daya in ban da mutum guda. Rahotannin da RSF suka fitar ya bayyana cewa babu gini ko da guda da ya rage a kauyen bayan mutuwar dukkan mazauna yankin sama da mutum dubu daya.
Karin bayani:Kwalara ta salwantar da rayuka a Sudan
Galibin mazauna tsaunukan Marra sun kaurace wa yakin da aka shafe lokaci mai tsawo ana gwabzawa tsakanin sojojin Sudan da dakarun rundunar kar-ta-kwana ta RSF, inda suke rayuwa a cikin wani yanayi na yunwa da kuma rashin magunguna.