Zaben shugaban hukumar AU ya dauki hankalin jaridun Jamus
February 21, 2025Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta wallafa sharhi mai taken "Jami'in diflomasiyyar Afirka". Jaridar ta ce duk da cewar Mahmoud Ali Youssouf na daya daga cikin fitattun wadanda suka nemi matsayin shugaban hukumar zartarwa na Kungiyar Tarayyar Afirka AU, amma ya kasance abin mamaki ga mahalarta taron kungiyar da aka yi a Addis Ababa lokacin da aka ayyana ministan harkokin wajen Djibouti, a matsayin wanda ya yi nasara. Djibouti karamar kasa ce, inda da kadan ta fi jihar Hessen mai yawan jama'a sama da miliyan daya a nan tarayyar Jamus. Kuma Youssouf mutum ne wanda ba a san shi ba, idan aka kwatanta da babban abokin hamayyarsa Raila Odinga, wanda ya yi fice a siyasar Kenya da ma gabashin Afirka.
Karin bayani: Kungiyar AU ta dakatar da Nijar
Amma duk da haka 33 daga cikin shugabanni da gwamnatocin Afirka 49, suka kada kuri'ar amincewa da shi a matsayin mutumin da ya dace da wannan muhimmin aiki. A shekarar 2002 ne dai aka kafa kungiyar ta AU, da manyan manufofi, ciki har da hada kan kasashe mambobi da karfafa tare da kare martabarsu. Bugu da kari hakkin kungiyar AU ne ta tabbatar da zaman lafiya da tsaro da kwanciyar hankali. Sai sai bisa dukkan alamu, tarayyar Afirkar ta yi nisa daga wadannan manufofin. Rikice-rikice na kara kamari a fadin nahiyar, musamman ma yakin basasar da ake fama da shi a halin yanzu a Sudan da gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. Rigingimun da suka janyo wa AU suka daga bangarori daban-daban.
Ana tauye hakkin dan Adam a gabashin Kwango
A game da wadannan tashe-tashen hankula da ke ci gaba da mamaye wasu sassan Afirka ne dai, jaridar die tageszeitung ta yi sharhi a kan yadda Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin kan mummunan tasirin rikicin Kwango a kan al'ummar yankin gabashin kasar. A cewar babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya, 'yan tawayen M23 da Ruwanda suna amfani da karfi wajen cin zarafin jama'a, kuma dole ne a mutunta dokokin kasa da kasa a gabashin Kwango.
A cewar hukumar kare hakkin bil adama ta MDD, ana samun karuwar tashe-tashen hankula a kan al'ummar gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, kuma wajibi ne 'yan tawayen M23 da Ruwanda su daina wannan rikici da suke yi, kuma su bi dokokin jin kai na kasa da kasa. A cewar babban kwamishinan hukumar a Geneva, ya zamanto wajibi a bai wa fararen hula kariya ta musamman, ta hanyar gano bakin zaren warware wannan rikici da ke barazana ga ilahirin kasar.
Karin bayani: Ilimi ya tabarbare sakamakon rikici a gabashin Kwango
Cikin wani bayani da MDD ta wallafa, rayuwa da al'amura a gabashin Kwango na ci gaba da tabarbarewa, inda mayakan na M23 ke aikata munanan laifukan take hakkin bil'adama, kamar kashe-kashe da suka hada da kananan yara da cin zarafin mata ta hanyar tilasta su yin jima'i. Kazalika, hare-hare kan asibitoci da sansanonin ‘yan gudun hijira na karuwa. MDD ta ce dubban mutane sun rasa matsugunansu, a yayin da aka kama wasu matasa 'yan Kwango ba bisa ka'ida ba, aka tsare su da kuma wulakanta su yayin da suke gudun hijira, daura kuma da tilasta wa mutanen komawa inda suka fito.
Mayakan RSF na kashe fararen hula a Sudan
Ita kuwa jaridar Zeit Online sharhi ta rubuta mai taken "Tashe-tashen hankula a Sudan" :daruruwa mutane ne suka mutu a harin da mayakan sa kai na RSF suka kai wa fararen hula a Sudan. A cewar wata kungiyar kare hakkin bil'adama ta kasar Sudan, sama da mutane 200 ne aka kashe a wani hari da mayakan RSF suka kai wasu kauyuka biyu na jihar White Nile cikin kwanaki uku da suka gabata. Akwai yara da mata na daga cikin wadanda suka mutu. Har ila yau harin ya yi sanadiyar kashe mutane da yin garkuwa da mutane da kuma kwace.
Karin bayani: Yunkurin lalubo mafita ga rikicin Sudan da ke kara faskara
Kungiyar ta lauyoyin gaggawa da ke tattara bayanan take hakkin dan adam, ta bayyana harin da aka kai kan mazauna kauyuka biyu na Al-Kadaris da Al-Chalwat da ke kudancin Sudan a matsayin kisan kare dangi. An harbe mazauna kauyukan da suka tsere a lokacin da suke kokarin tserewa ta kogin Nilu, wasu kuma sun nitse a cikin ruwa. Shaidu daga kauyukan biyu sun bayyana cewa, dubban mutane ne suka tsere daga gidajensu a lokacin harin, wanda ya dauki tsawon kwanaki. Miliyoyin 'yan Sudan ne suka tsere wa wannan rikici da ke ci gaba da gudana tsakanin manyan hafsoshin kasar, a kan dalilai na neman kakkange madafan iko.