Za a rusa majalisar dokokin Thailand
September 3, 2025Yunkurin rusa majalisar dokokin Thailand na nuna cewa, akwai yiwuwar gudanar da sabon zabe a kasar zuwa nan da karshen wannan shekarar nan ta 2025. A ranar Juma'ar da ta gabata ce kasar ta fada cikin rikici na siyasa da ma rashin wani tsayayyen shugaba, sakamakon tsige firanministar kasar, Paetongtarn Shinawatra da kotun kundin tsarin mulkin kasar ta yi bisa zarginta da karya wasu ka'idoji.
Kawo yanzu dai, jami'iyyarta ta na ci gaba da mulkar kasar na wucin gadi tare da fatan samun nasara a zabe kan babbar jam'iyyar adawa ta People's Party da dan takararta Anutin Charnvirakul, dan kasuwa mai ra'ayin rikau. Masu sharhi na cewa, gudanar da sabon zabe a kasar shi ne mafita ga rikicin siyasar saboda da kamar wuya a iya kafa ingantanciyar gwamnati.