An ga watan Karamar Sallah a Saudiyya
March 29, 2025Hukumomin Saudiyya sun sanar da cewa za a gudanar da Karamar Sallah ko kuma Eidil Fitir a kasar a gobe Lahadi, bayan ganin jinjirin watan Shawwal a dazu dazun nan wanda ke kawo karshen ibadar Azumin Ramadan da Musulmi da suka share kwanaki 29 suna yi a bana.
Hakazalika kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Qatar suma sun fidda sanarwar cewa za a hau idin Karamar sallar a gobe Lahadi, yayin da kasar Iran da Daular Omman da ke da rinjayen mabiya Shi'a su kuma suka ce za a gudan da sallar a ranar jibi Litinin.
Za a gudanar da bukukuwan Sallar ta bana ne a cikin yanayi na tashin hankali da sake kunno kai a yankin Gabas ta Tsakiya, inda Isra'ila ta sake kai farmaki a zirin Gaza na Falasdinu da nufin kawar da kungiyar Hamas, lamarin da ya yi ajalin gwamman mutane kamar yadda ma'aikatar lafiya ta Gaza ta bayyana.