Za a binne Edgar Lungu a Zambiya
August 8, 2025An kwashe tsawon watanni biyu ana takaddama kan birnin marigayin, inda gwamnatin Zambiya ta nemi ta yi mishi jana'izar ban girma, yayin da iyalansa kuma ke son a birne shi a Afirka ta Kudu. Mai dakin marigayin da kuma 'ya'yansu ne suka yi uwa da makarbiya wajen hana kai gawarsa zuwa Zambiya inda suka ce, ba zai so shugaban kasar mai ci kana abokin hamayyarsa, Hakainde Hichilema ya kasance a wurin taron birni shi ba.
Karin bayani:Edgar Lungu na Zambiya ya riga mu gidan gaskiya
Sai dai kotun da ke birnin Pretoria, ta ce wasiyyar tsohon shugaban kasar da kuma bukatar iyalansa ba za su sha gaban ikon kasar ba. Kotun ta kuma umurci iyalan Lungu su mika gawarsa ga hukumomin Zambiya. Marigayi Edgar Lungu ya mutu a ranar 5 ga watan Junin 2025 a kasar Afirka ta Kudu yana da shekaru 68. Ya hau kan karagar mulkin Zambiya ne a shekarar 2015, sai dai ya sha kaye a hannun Shugaba Hichilema a zaben shekarar 2021. Tun daga wancan lokacin iyalansa ke fuskantar zarge-zargen cin hanci.