Zaɓukan shugaban ƙasa da majalisa a Nijar
January 31, 2011Talla
Yau Litinin aka fara zaɓen shugaban ƙasa da na majalisar dokoki a Jamhuriyar Nijar. A dangane da haka mun tanadar muku da rahotanni daga wakilanmu Salissou Boukari daga Tahoua, da Salissou Kaka daga Maraɗi, da Larwana Malam Hami daga Damagaram, da kuma Tila Amadou daga Agadas. Za ku iya sauraron waɗannan rahotanni daga ƙasa.