Zaɓen shugaban ƙasa a Rasha
March 3, 2012Ma'aikatar kula da harkokin cikin gidan na Rasha ta ƙara da cewar domin kare yiwuwar ƙaddamar da harinn ta'addanci, ta kuma wadata runfunan zaɓe a manyan biranen ƙasar da na'urorin gano makamai, a yayin da al'ummar Rasha kimanin miliyan 110 ke zaɓen shugaban ƙasar da zai maye gurbin shugaba Dmitry Medvedev inda ake ganin Vladmir Putin zai kai gaci a fafutukar dake tsakanin 'yan takara biyar domin ɗarewa bisa kujerar shugabancin ƙasar ta Rasha, bayan daya taɓa riƙe muƙamin a tsakanin shekara ta 2000 da kuma 2008.
Zaɓen shugaban na Rasha a wannan Lahadin dai, ya zo ne a dai dai lokacin da wasu 'yan ƙasar suka kwashe tsawon watanni ukku suna gudanar da zanga zangar neman tabbatar da bin tafarkin dimoƙraɗiyya da kuma gudanar da zaɓe cikin 'yanci da walwala a sassa daban daban na biranen ƙasar, abinda wasu ƙwararru da kuma 'yan siyasa suka fassara da cewar, a yanzu ƙungiyoyin kare haƙƙin jama'a sun farka da barcin da suka daɗe suna yi ne na kusan shekaru 10.
A cewar Natalia Taubina, darektar wata ƙungiyar farar hula dake fafutukar tabbatar da adalci a Rasha, kana mamba a cikin ƙawancen ƙungiyoyin farar hula na Turai da Rasha, tafarkin da Putin ya bi wajen sanar da takarar ta sa ne ta ɓatawa 'yan ƙasar rai, sakamakon abubuwan da suka biyo bayan ayyana kansa a matsayin wanda zai gaji Medvedev:
" Ta ce, babban abinda ya harzuƙa Rashawa shi ne maguɗin da aka tafka a lokacin zaɓukan 'yan majalisar dokokin daya gudana a Rasha cikin watan Disamba, kana da kasancewar hatta 'yan ƙasar da suka sanya ido akan zaɓukan don raɗin kansu, sun shaida maguɗin."
Sai dai kuma hukumar zaɓen ƙasar ta Rasha ta ce a wannan Asabar ce ta yi gwajin na'urorin bayar da bayanai da kuma nuna hotuna kai tsaye daga rumfunan 96,000, abinda Mr Putin ya ce ke da nufin hana tafka maguɗin zaɓe ne, amma 'yan adawa suka ce na'urori kaɗai ba za su hana tafka maguɗi ba.
Dama dai tun cikin watan Satumba ne Firaminista Putin da kuma shugaba Medvedev suka sanar da cewar cimma matsayar cewar Putin zai naɗa Medvedev ɗin a matsayin firaminista idan ya sake ɗare kujerar shugabancin Rashar, lamarin da Mikhail Kasyanov, jagorar adawa kana tsohon firaminista a ƙasar ta Rasha ya ce shi ne ya ingiza rukuni daban daban na Rashawa hawa kan tituna domin nuna bore:
" Ya ce, a yanzun nan da ake batu a Rasha akwai ɗimbin matsaƙaitan masu samun kuɗaɗen shiga da kuma masu arziƙin dake gudanar da zanga- zangar neman kare 'yancin su da kuma tanade-tanaden tsarin mulkin ƙasar su ciki kuwa harda 'yancin mutunta zaɓuka cikin gaskiya da adalci."
Tun a jajiberin zaɓen shugaban ƙasar Rashar ne dai, shugaba mai ci a yanzu Dmitry Medvedev ya buƙaci 'yan ƙasar da su fito ƙwansu da ƙwarƙwatar su domin kyautata abinda ya ƙira makomar ƙasar Rasha cikin 'yan ci da walwala da kuma ci gaba.
Zaɓen na Rasha dai ya zo ne a dai dai lokacin da ƙasar ke yin fito na fito tare da sauran ƙasashen yammacin duniya game da rikicin dake ci gaba da wanzuwa a Siriya da kuma taƙaddama akan shirin nukiliyar Iran.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe
.