Yunkurin sace Saadi Gadhafi daga Nijar
October 2, 2012Sai dai duk da cewa yunkurin ya ci tura batun ya soma haifar da ce-ce-ku-ce a kasar bayan da wasu rahotanni su ka zargi wasu mambobin gwamnati da ma wani dan majalisar dokoki da cewa akwai hannunsu a cikin shirin. Wani bincike da gidan rediyon DW ya gudanar akan wannan lamari ya gano cewa ranar Asabar, 22 ga watan Satumban da ya gabata ne wani jirgi sanfulin "Jet" mallakar wani kamfanin kasar Afrika ta Kudu da ke dauke da matuka 'yan asalin kasar Turkiyya ya sauka ba zato ba tsammani da karfe biyar da minti biyar na yammacin wanann rana a babban filin saukar jiragen sama na Diori Hamani da ke a birnin Yamai.
Shin da sanin gwamnati?
Da jami'an tsaro na filin jirgin su ka tunkari mutanen da ke cikin jirgin wadanda suna magana ne a cikin harshen Inglishi sun shaida masu cewa sun zo ne domin tafiya da Saadi Gadhafi kuma su ka bayyana sunayen wasu mambobin gwamnati guda biyu da wani dan majalisar dokoki a matsayin abokanin huldarsu a cikin wanann shiri. Boukari Zilli na daga cikin jerin mutanen da rahotanni su ka ruwaito cewa mutanen da su ka zo daukar Saadi Gadhafi sun ambato. Sai dai a firar da ta hada shi da gidan rediyon DW dan majalisar ya musanta zargin.Yanzu haka dai rahotanni da wasu mujallu ke yadawa kan wanann batu da ba mu tabbatar da sahihancinsu ba na bayyana cewa jirgin da ya zo ne da niyyar ficewa da Saadin zuwa kasar Zimbabwe inda yake sa ran samun garkuwa daga hukumomin wanann kasa wadanda tun a farko su ka nuna adawarsu da yakin kasar ta Libiya da ya kai ga yin sanadiyyar mutuwar Gadhafi. Tuni dai kungiyoyin farar hular kasar ta Nijar su ka soma tofa albarkacin bakinsu kan wannan batu.
Gwanmati ta ki ta ce uffan
Har ya zuwa yanzu dai babu wasu bayanai a hukumance da gwamnatin Nijar din ta ba da kan wannan lamari da ma yanda aka yi jirgin da ya zo da mutane da ke a cikinsa su ka fice daga kasar. Shi dai Saadi Gadhafi wanda Nijar ta bai wa mafaka da sunan jin kai na ci gaba da kasancewa wani bakon alkakai da ke ta faman neman hanyoyin da za su bashi damar ficewa daga kasar ta Nijar- abun da kuma wasu ke ganin na iya haifar da sabanin diplomasiyya da ma lalata zaman arba da ake yi a halin yanzu tsakanin gwamnatin kasar ta Nijar da ta gwamnatin kasar Libiya mai ci a yanzu.
Za ku iya sauraron sautin wannan rahoto daga kasa.
Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Halima Balaraba Abbas