An nemi hukunta masu satar mai a Najeriya
September 20, 2022A yayin jawabinsa na farko tun bayan dawowa daga dogon hutun da majalisun kasar suka yi, kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, ya ce, laifin satar mai, daidai ya ke da laifin cin amanar kasa, yana mai kira kan daukar tsatsauran mataki da zai yi tasiri a shawo kan matsalar a Najeriya.
Yan Majalisun da suka tafi hutu bayan da suka fusata da matsalar tabarbarewar tsaro a Najeriya, sun bukaci a samar da dokar don ceto tattalin arzikin Najeriya daga barazanar da ya ke fuskanta na durkushewa a sakamakon matsalar.
A watan Afrilun bana, kiyasin gwamnatin kasar ya nunar da cewa, an sace man da ya kai darajar dala biliyan uku, kuma daya daga cikin hanyoyin da aka tafka wannan asara, shi ne ta hanyar fasa bututun man gwamnatin. Yankin Naija Delta na daga cikin yankunan kasar da ya yi kaurin suna a sata dama tace man ta haramtacciyar hanya.