Yaƙin neman zaɓe a Nijar
January 21, 2011Talla
Mako guda bayan ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na majalisar dokoki a Jamhuriyar Nijar, har yanzu shiru ka ke ji a wasu sassa na wannan ƙasa, saboda cewa babu wani taron gangami ko wani abu da ke nuni da ga armashin yaƙin na neman zaɓe. A sakamakon haka ana bayyana shakku game da yiwuwar gudanar da zaɓukan a ranakun da aka shirya.
Wakilinmu, Mahamane Kanta daga Yamai da kuma Salissou Kaka, daga Maraɗi sun aiko mana da rahoto. Za ku iya sauraron sautinsu a ƙasa.