UNCHR: 'Yan gudun hijira daga Afirka na karuwa
June 20, 2025Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR ta ce kaso 80 cikin 100 na wadannan mutane da suka bar gidajensu sakamakon rikici ko sauyin yanayi mata ne da kananan yara, to amma wasu kan koma gida da zarar an dan samu sarara wa daga tashin hankalin da ya tilasta musu barin gidajen nasu. Babban jami'in hukumar mai kula da shiyyar yammaci da tsakiyar Afirka, Abdouraouf Gnon-Konde ya tabbatar da hakan. Kasashen da wannan balahira ta fi kamari sun hadar da Sudan da Chadi da Najeriya da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Burkina Faso da Mali da kuma Kamaru, inda kiyasi ya nuna cewa mutane miliyan 12 da dubu 700 ne ke fuskantar wannan mummunan yanayi na rayuwa.
Karin Bayani: Fargaba kan makomar 'yan gudun hijira
Ga misali Chadi da ke zama mafakar wadanda suka tsere daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Jamhuriyar Nijar, yanzu haka tana fama da tururuwar mutanen da ke shiga daga makwabciyarta Sudan sakamakon yakin basasa na sama da shekaru uku da adadinsu ya kai mutane dubu 780. To amma babbar jami'ar Hukumar Kula da Kaurar Jama'a ta Majalisar Dinkin Duniya IOM mai kula da wannan shiyya Luisa de Freitas ta ce, dubu 300 daga cikin mutanen da suka koma daga Sudan din 'yan asalin Chadi ne da ke rayuwa a Sudan shekaru aru-aru.
A gefe guda kuma kaso 80 cikin 100 na 'yan gudun hijirar yankunan biyu, sun fito ne daga kasashen Najeriya da Burkina faso da kuma kamaru sakamakon hare-haren ta'addancin kungiyoyi masu ikirarin jihadi da na 'yan bindiga da ibtila'in ambaliyar ruwa da kuma annobar farin dango. Domin rage wannan adadi na mutane masu gararambar neman mafaka a sanadiyyar afkuwar masifu a garuruwansu Majalisar Dinkin Duniya ta fara aikin mayar da wasu muhallansu da amincewarsu, inda ta mayar da mutane dubu 194,200 gida a kasar Mali da wasu dubu 64,700 Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Ga wadanda suka bar kasashensu na asali kuwa, mutane dubu 11 ne kacal suka amince da komawa gida daga kasashen Najeriya da Mali da kuma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Karin Bayani: 'Yan gudun hijira na zaman kunci a Libiya
A nasa bangaren, mai magana da yawun ofishin Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR da ke birnin Dakar na Senegal Alpha Seydi Ba ya ce, babban tushen wadannan masifu da ke damun Afirka bai wuce siyasa ba. A cewarsa idan aka gyara wannan bangare aka samar da kyakkawan tsari, to wadannan mutane za su samu damar komawa gida domin babu wanda zai bar muhallinsa haka siddan bisa radin kansa. A halin yanzu dai, wannan hukuma na fama da matsalar karancin kudin gudanarwa, inda aka rage adadin da ake ware wa bangarensu da kaso 50 cikin 100 a bana.