Najeriya: Yaushe rashin tsaro zai zo karshe?
June 3, 2025Wani rahoto da kungiyar kasa da kasa ta The International Society for Civil Liberties and Rule of Law ta fitar ne, ya nunar da cewa akwai sassa 950 cikin surkukin dazuzzukan yankin Kudu maso Gabashin Najeriya da 'yan fashin daji da masu satar mutane da Fulani makiyaya ke a bobboye suna aikata muggan laifuka na tayar da zaune tsaye. Kungiyar ta Int'l Soc For Civil Liberties and Rule Of Law, ta kuma zargi gwamnonin yankin da nuna halin ko in kula.
Karin Bayani: An kashe manoma 14 a Arewa maso gabashin Najeriya
Kungiyar ta kasa da kasa ta ce daga cikin laifukan da awadannan miyagu ke aikatawa a dazuzzukan Najeriya, har da kisa da kai farmaki kan jama'a. To sai dai fa kuma Barista Abdullahi Jalo da ya kasance Bafulatani, ya wanke Fulanin Najeriyar da shiga cikin jerin wadanda ake magana na aikata mugagn laifuka a yankin na Igbo. A wani labarin kuma bayanai daga rundunonin tsaron soji da na jami'an tsaro na farin kaya DSS a kasar suka nunar da cewa sun kama wata babbar mota makare da makamai da aka yi niyyar kai su ga sansanin 'yan rajin kafa kasar Biafra na kungiyar IPOB a yankin na Igbo.
Bayanan sun nunar da cewa, yawan makaman ya kai dubu 164 da aka nufi kai wa kungiyar ta IPOB da ke karkashin Nnamdi Kanu da har yanzu yake tsare a hannun hukumomin Najeriyar kan tuhumar cin-amanar kasa. An dai kama motar a tsakanin hanyar Asaba babban birnin jihar Delta zuwa birnin Onitshaa jihar Anambra. Rundunar tsaron dai ta ce ta ga kama wasu mutane da a yanzu suke taimaka mata da bayanai kan makamai da aka tabbatar an sayo su ne daga kasar Ghana.
Karin Bayani: 'Yan IPOB na kuntata wa jam'a a Ebonyi da Abia
Matsalolin tsaro dai yanzu a Najeriya na kan gaba cikin matsalolin da suka addabi al'umma a kasar, baya ga yawaitar barbazuwar kananan makamai ba bisa kaida ba. Ko a baya-bayan nan ma sai da kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta fitar da rahoton cewar, cikin shekaru biyu da kama mulkin Shugaba Bola Ahmad Tinubu na jamiyyar APC kimanin mutane dubu 10 ne suka halaka sakamakon ayyukan 'yan fashin daji da 'yan ta'addan Boko Haram da kuma tashin hankula na kabilanci a kasar.